Bikin nuna kayan ƙawa da wasan zamiyar teku a hotunan Afirka na wannan mako

An wallafa

Zaɓabbun hotuna masu ƙayatarwa daga sassan Afirka a wannan makon:

.

Asalin hoton, KIM LUDBROOK/EPA

Bayanan hoto, Wata mai wasan zamiyar teku tana tsunduma cikin ruwa yayin da rana ta buɗe a gaɓar gabashin Afirka ta Kudu ranar Lahadi.
.

Asalin hoton, FRANCOIS G DURAND/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Wata fitacciyar ƴar Fim ƴar asalin Faransa kuma mazauniyar Guinea Fatoumata Guinea Kaba kan jan kapet a bikin haska fina-finai ranar Juma'a...
.

Asalin hoton, DANIELE VENTURELLI/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Ga kuma fitacciyar ƴar ƙawa Halima Aden ƴar asalin Somalia wadda ta karɓi kyautar ƙarfafa wa mata gwiwa a bikin bayar da kyaututtuka na World Influencers and Bloggers Awards (Wiba).
.

Asalin hoton, MOHAMED MESSARA/EPA

Bayanan hoto, A ranar Asabar ne, wani baƙo ke duba zane-zanen Mohamed Ben Methaf yayin bikin bajekolin ayyukan zane-zane na Carthage Contemporary Art Days Festival a babban birnin Tunisia.
.

Asalin hoton, RONEN ZVULUN/REUTERS

Bayanan hoto, Ranar Lahadi kuma, ƴan Isra'ila da tsatsonsu Habasha ne riƙe da hotunan ƴan uwansu yayin wata zanga-zanga a birnin Ƙudus inda suke neman gwamnati ta daina hana ƴan Habasha masu bin addinin Yahudawa shiga Isra'ila.
.

Asalin hoton, ANDRE KOSTERS/EPA

Bayanan hoto, A Guinea Bissau, magoya bayan Domingos Simoes Pereira da ƙungiyarsa ta Inclusive Alliance Platform sun yi gangami ranar Litinin a babban birnin ƙasar gabanin zaɓen 4 ga watan Yuni.
.

Asalin hoton, MOHAMED ABD EL GHANY/REUTERS

Bayanan hoto, A ranar Asabar, tawagar masu kaɗe-kaɗe daga Masar na nuna iyawarsu a bikin kaɗe-kaɗe na International Festival for Drums and Traditional Arts a Cairo, babban birnin ƙasa.
.

Asalin hoton, DEMIAN ALDAY ESTEVEZ/EPA

Bayanan hoto, A irin wannan ranar, wata mai goyon bayan ƙwallon ƙafa ke bai wa Senegal ƙwarin gwiwa a wasanta da Colombia a gasar cin kofin duniya ta ƴan kasa da shekara 20 a birnin La Plata da ke Argentina. An ƙare wasan da kunnen doki.
.

Asalin hoton, OLUKAYODE JAIYEOLA/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, An rantsar da Bola Tinubu a matsayin Shugaban ƙasar Najeriya a wani biki da aka yi a Abuja ranar Litinin, inda ya yi alƙawarin magance matsalar tsaro da inganta tattalin arziki.
.

Asalin hoton, ZOHRA BENSEMRA/REUTERS

Bayanan hoto, Rikici ya ɓarke a Dakar, babban birnin Senegal a ranar, tsakanin ƴan sanda da magoya bayan Ousmane Sonko. A cikin makon ne kuma aka yanke wa madugun ƴan adawar hukuncin ɗaurin shekara biyu a gidan yari.
.

Asalin hoton, JALAL MORCHIDI/EPA

Bayanan hoto, An kammala bikin nuna kayan ƙawa na al'ada a Rabat inda aka ƙare da kayayyakin da Fadila El Gadi ta ɗinka.
.

Asalin hoton, PHILIPPE LOPEZ/AFP

Bayanan hoto, Rana kuma ta faɗi a tsibirin Mayotte na tekun Faransa da Indiya wanda ya soma aikin tisa ƙeyar ƴan ci-rani, akasarinsu sun fito daga Comoros mai maƙwabtaka.