Man United ta taya Hojlung, Juventus na son Lukaku

An wallafa

Manchester United ta yi wa Atlanta tayin fatar baki na fan miliyan 42.8 da ƙarin fan miliyan 8.5 kan ɗan wasanta mai shekara 20 ɗan Denmark Rasmus Hojlund. (Athletic - subscription required)

Daraktan wasanni na Juventus Cristiano Giuntoli zai yi tattaki zuwa Ingila domin tattaunawa da Chelsea don neman aron ɗan wasanta mai shekara 30 Romelu Lukaku.(Calciomercato, via Goal)

Lukaku na Landan yayin da sauran 'yan wasan ƙungiyar suke Amurka wajen buga wasannin share fara kakar wasanni. (Times - subscription required)

Dan wasan Faransa da PSG Kylian Mbappe bai nuna sha'awar tattaunawa da wakilan Al-Hilal ba game da komawarsa Saudiyya da taka leda. (Sky Sports)

Wata majiya da ke kusa da masu tattaunawa kan ɗan wasan ta bayyana cewa ya amince da wasu sharuɗa na komawa Real Madrid baɗi. (Telegraph - subscription required)

Da alama Chelsea za ta haƙura da ɗan wasan tsakiyar Argentina Paulo Dybala - bayan ɗan wasan mai shekara 29 ya sabunta kwantaraginsa da Roma.(Tuttomercatoweb, via Football Transfers)

Itama West Ham gab take da haƙura da ɗan wasan Ingila mai shekara 23 Conor Gallagher, bayan da ya nuna yana son ci gaba da zama a Chelsea, ya nemi hannu a ƙarƙashin sabon koci Mauricio Pochettino. (Mail)

A gefe guda dai Hammers ɗin na ci gaba da taya ɗan wasan Southampton James Ward-Prowse, mai shekara 28, wanda kuma ake sa ran cinikin zai yi wu. (Football Insider)

Al-Hilal na ci gaba da tattaunawa da PSG kan ɗan wasan Italiya Marco Verratti mai shekara 30. (Fabrizio Romano)

Dan wasan PSG ɗan Portugal Renato Sanches mai shekara 25, na dab da komawa Roma a matsayin aro.(L'Equipe - in French)