West Ham ta kammala cinikin Maguire da Ward-Prowse

An wallafa

West Ham United ta cimma matsaya kan sayen Harry Maguire na Manchester United da James Ward-Prowse na Southampton kan kudi kusan fan miliyan 60.

Maguire, mai shekara 30, ya yi fama da rashin samun damar buga wasa a Old Trafford a kakar wasan da ta wuce, an kuma cire shi daga mukamin kyaftin a kakar wasa ta bana.

An fahimci cewa yana sha'awar tafiya duk da cewa ba a kammala kulla yarjejeniyar sharudda ba, amma ba a tsammanin hakan zai zama matsala.

Maguire ya koma United ne a watan Agustan 2019 kan fam miliyan 80, wanda shi ne dan wasan baya da ya fi tsada a duniya.

West Ham dai na ta kokarin daukar Ward-Prowse a bazaranar nan amma Southampton, wadda ta koma gasar Championship a kakar da ta gabata, ta ki amincewa har zuwa wannan lokacin.

Sai dai da alama cewa babu makawa Southampton ta rasa kyaftin din ta kuma yanzu tafiyarsa ta kusa tabbata.

West Ham na neman karfafa tawagar 'yan wasanta, bayan ta sayar da dan wasan tsakiya na Ingila Declan Rice ga Arsenal kan fan miliyan 105 da kuma dan wasan Italiya Gianluca Scamacca ga Atalanta kan fan miliyan 21.5.

Kocin Hammers David Moyes yana gab da siyan Edson Alvarez na Ajax a matsayin wanda zai maye gurbin Rice sannan kuma ana alakanta shi da neman Scott McTominay na Manchester United.

Maguire ya buga wa United wasanni 30 a kakar wasan da ta wuce, amma ya buga wasanni takwas kawai a gasar Premier.