Varane zai taka leda karkashin koci Fabregas a Como

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon ɗan wasan tawagar Faransa, Raphael Varane ya koma ƙungiyar Como, wadda za ta buga Seria A ta Italiya a bana.
Dan wasan mai shekaru 31 ya kasance bai da ƙungiya, bayan da kwantiraginsa ya kare a Manchester United, bayan kammala kakar da ta wuce.
Ya rattaba hannu kan yarjejeniyar shekara biyu da ƙungiyar ta Italiya.
Dan wasan wanda ya lashe gasar cin kofin duniya a 2018 ya ɗauki kofin La Liga uku da na zakarun Turai hudu a Real Madrid, sannan yayi kaka uku Old Trafford.
Ya kuma buga wa Faransa wasa karo 93 daga baya ya yi ritaya daga buga wa tawagar tamaula.
Como, wadda za ta koma buga babban gasar Italiya bayan shekaru 21, ta naɗa tsohon dan wasan Arsenal da Chelsea, Cesc Fabregas a matsayin kocinta.
"Zan sake haduwa da Cesc, amma wannan karon ba a matsayin abokin hamayya ba," in ji Varane.





