Real Madrid na atisayen tunkarar Rayo a La Liga

An wallafa

Real Madrid ta fara shirin karbar bakuncin Rayo Vallecano, domin buga wasan mako na 12 a gasar La Liga ranar Lahadi a Santiago Bernabeu.

Kungiyar da Carlo Ancelotti ke jan ragama tana matakin farko a teburin La Liga da maki 28, iri daya da na Girona, wadda take biye da ita.

Ita kuwa Rayo mai mai maki 17 tana ta takwas din teburi a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

Sabon dan wasan da Real Madrid ta dauka kan fara kakar bana, Jude Bellingham shi ne kan gaba a cin kwallaye a gasar mai 10 a raga, bayan wasa 11.

Real ta fara atisaye da yin guje-guje, daga nan kowa ya dauki tamaula yana motsa jiki da shi.

'Yan wasan sun kammala motsa jiki da raba kwallo a rabin fili, inda suka dunga bani in baka da kuma gwada mai tsaron raga.

Ceballos da Mendy sun yi nasu atisayen a dakin motsa jiki daga baya suka fito filin wasan.

Wasan da suka yi a bara tsakanin Real da Rayo:

Sifanish La Liga Laraba 24 ga watan Mayun 2023

  • Real Madrid 2 - 1 Rayo Vallecano

Sifanish La Liga Litinin 7 ga watan Nuwamba 2022

  • Rayo Vallecano 3 - 2 Real Madrid

Wasannin mako na 12 da za a yi Asabar 4 ga watan Nuwamba:

  • Osasuna da Girona
  • Real Betis da Real Mallorca
  • Celta de Vigo da Sevilla
  • Real Sociedad da Barcelona