Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Aston Villa ta kammala ɗaukar Maatsen daga Chelsea
Aston Villa ta kammala ɗaukar ɗan wasan Chelsea, mai tsaron baya, Ian Maatsen kan £35m.
Maatsen, mai shekara 22, ya buga wasannin aro a Borussia Dortmund, wanda ya taka rawar da ƙungiyar ta kai wasan karshe a Champions League.
Yanzu haka yana tare da tawagar Netherlands a Euro 2024, wadda ke shirin buga zagaye na biyu da Romania ranar Talata a Jamus.
Shi ne na biyu da Aston Villa ta ɗauka a yanzu haka, bayan Lewis Dobbin daga Everton.
Chelsea ta ɗauki Maatsen a 2019 daga PSV Eindhoven, wanda ya taka rawar gani a lokacin da ta tura shi buga wasannin aro a Charlton Athletic da Coventry City da Burnley da kuma Dortmund.
Ya taka gagarumar rawar da ta kai Burnley ta samu gurbin shiga Premier League a 2022-23, wanda ya ci ƙwallo hudu a wasa 39, kuma yana cikin fitattun ƴan wasa a gasar ta Championship.
Maatsen ya fara buga wasanni a kakar 2023/24 a zagayen farko a Chelsea, amma sai ya kasa samun gurbi karkashin koci, Mauricio Pochettino, duk da yin wasa 15 a dukkan fafatawa.
Daga nan aka bayar da aronsa ga Dortmund a watan Janairu, bayan da ya tsawaita ƙwantiragin kaka daya da ƙungiyar Stamford Bridge.
A lokacin da ya taka leda a Jamus, Maatsen ya yi karawa 23 da cin ƙwallo uku, inda Dortmund ta kare a mataki na biyar a Bundesliga, wadda Real Madrid ta doke ta 2-0 ta ɗauki Champions League.
Ya bar Stamford Bridge bayan buga wasa 16 a ƙungiyar da ke yammacin London.