Ƴan Real Madrid da za su buga mata wasan sada zumunta a Amurka

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Real Madrid ta sanar da ƴan wasan da za su buga mata wasannin sada zumunta a Amurka, domin shirin tunkarar kakar 2024/25.

Ƙungiyar da ke buga babbar gasar tamaula ta Sifaniya, mai rike da La Liga da Champions League a bara, za ta kara da AC Milan da Barcelona da kuma Chelsea.

Tuni Real Madrid ta bayyana sunan ƴan wasan da ta je da su Amurka, amma banda waɗanda suka buga wasannin daf da karshe a Euro 2024 da Copa America.

Hakan ya sa Dani Carvajal da Ferland Mendy da Bellingham da Fade Velverde da Aurelien Tchouameni da Eduardo Camavinga da Kylian Mbappe ke hutu.

An kuma ce sai ranar 7 ga watan Agusta za su koma Real Madrid ya rage sauran mako ɗaya tsakani ta kara a European Super Cup da Atalanta a Warsaw a Poland.

Har yanzu David Alaba na iinya, kenan ba zai je Amurka domin buga wasannin sada zumuntar ba.

To sai dai Real Madrid ta je Amurka da sabon ɗan wasan da ta ɗauka Endrick daga Palmeiras.

Wasannin da Real Madrid za ta buga a Amurka

31 ga watan Yuli - Real Madrid da AC Milan a Soldier Field, Chicago

3 ga watan Agusta - Barcelona da Real Madrid a MetLife Stadium, New Jersey

6 ga watan Agusta - Chelsea da Real Madrid a Bank of America Stadium, Carolina.

Ƴan wasan Real Madrid:

Masu tsare raga: Courtois, Lunin and Fran González.

Masu tsare baya: Militão, Lucas Vázquez, Vallejo, Fran García, Rudiger, Jacobo Ramón, Lorenzo, Obrador, Asencio and Joan Martínez.

Masu buga tsakiya: Modrić, Arda Güler, Ceballos, Nico Paz, Mario Martín, Palacios and Jeremy de León.

Masu cin ƙwallaye: Vini Jr., Rodrygo, Endrick, Brahim, Latasa and Álvaro Rodríguez.