Carvajal ya buga wa Real Madrid wasa na 400

An wallafa

Carvajal ya buga wa Real Madrid wasa na 400 ranar Lahadi a gasar La Liga da Real Madrid ta tashi 1-1 da Atletico Madrid.

Kungiyoyin da ke birnin Madrid, sun buga karawar ta hamayya a wasan mako na 23 a Santiago Bernabeu a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

Brahim Diaz ne ya fara ci wa Real kwallo a minti na 20 da take leda, daga baya Atletico ta farke daf da za a tashi daga fafatawar ta hannun Marcos Llorente.

Carvajal ya yi wadan nan wasannin a kaka ta 11 a Real Madrid, wanda aka yi nasara da shi a fili sau 272 da cin kwallo 11 da daukar kofi 23.

Cikin wasa 400 da ya yi wa Real ya yi mata guda 268 a gasar La Liga da 83 a Champions League da 25 a Copa del Rey.

Sauran sun hada da karawa takwas da ya yi a Club World Cup da wasa biyar European Super Cup da kuma fafatawa 11 a Spanish Super Cup.

Kakar tamaula da ya fi yawan buga wa Real Madrid wasanni ita ce ta 2013/14 da kuma 2022/23 da kowacce ya yi 45.

Kungiyar da ya fi yawan fuskanta ita ce Atlético Madrid, wadda ya hadu da ita karo na 31.