Matashin da ya sauya rayuwar jaririyar da mahaukaciya ta jefar a kasuwa

Matashin da ya sauya rayuwar jaririyar da mahaukaciya ta jefar a kasuwa
An wallafa

Wani matashi a Najeriya ya bayyana yadda ya tsinci wata jaririya a kasuwa bayan mahaifiyarta ta jefar da ita.

Matashin, mai suna Benkingsley Nwashara, dan Jihar Enugu, ya shaida wa BBC cewa ya tsinci jariryar ne bayan ta kwana uku a yashe ba tare da samun kulawa ba.

Ya kara da cewa daga nan ne suka kai ta ofishin 'yan sanda kuma daga nan suka kai ta asibit aka duba lafiyarta.

Ya ce an gano cewa tana fama da cutar rashin abinci an kuma yi mata magani daga nan ya tafi da ita gida.

Matashin ya kara da cewa babbar burinsa shi ne ya jariryar ta girma ta yi karatu domin taimaka wa al'umma.