Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan wasa ka iya fara yajin aiki saboda yawan wasanni - PFA
Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya Fifa ta yi gargaɗin cewa 'yan wasa sun bayyana aniyarsu ta fara yajin aiki idan aka ci gaba da wahalar da su da yawan wasanni.
Shugaban ƙungiyar ƙwararrun 'yan wasa ta Professional Footballers’ Association (PFA), Maheta Molango, na ganin an gama ƙure malejin 'yan wasan.
Da ma PFA ta daɗe tana kira a ɗauki mataki don rage cunkoso a kalandar wasanni, musamman a yanzu da za a gudanar da gasar Kofin Duniya na Kulob mai tawaga 32 a kaka mai zuwa.
"Na taɓa shiga ɗakin wani kulob da hakan ta faru da su kwana 10 da suka wuce, na ce musu: 'Zan so na zo nan na yi ɓaɓatu amma fa alhakin gaba ɗaya yana wuyanku ne. Wane irin shiri kuka yi?" in ji Molango lokacin da yake magana a taron ƙungiyar Fifpro da ya duba wahalar da 'yan wasa ke sha.
"Wasu daga cikinsu sun ce: "Ba zai yiwu ba, za mu iya fara yajin aiki.' Wasu kuma suka ce: 'mene ne amfanin hakan? Tabbas ni milioniya ne amma ba ni da lokacin da zan kashe kuɗin'.
"Ba fa ƙungiyar ce ma ta yi maganar ba, Jurgen Klopp da Pep Guardiola ne. Mun kai lokacin da ba za mu iya cewa komai ba."
Wani bincike da ya mayar da hankali kan matasan 'yan wasa ya gano yadda yawan buga wasa ke shafar jiki da kuma ƙwaƙwalwarsu.
Binciken ya ce Jude Belingham na Real Madrid mai shekara 20 ya buga minti 18,486 na wasanni, idan aka kwatanta da minti 3,929 da David Beckam ya buga, da kuma 6,987 da Frank Lampard ya buga lokacin da suke da irin waɗannan shekarun.
Tuni PFA ta yi barazanar kai ƙara kotu kuma ta ci gaba da duba yiwuwar yin hakan saboda yawan wasannin da ake tilasta wa mambobinta bugawa a ƙwallon ƙafa.
Bisa tanadin ƙungiyar ta PFA, an aika wa Fifa wasiƙa a watan Mayu, inda ita ƙungiyar masu lig-lig ta duniya ta yi barazanar ɗaukar mataki idan ba a janye maganar buga Kofin Duniya na Kulob mai tawaga 32 ba a ƙarshen kakar baɗi.