Wane ne Sergei Surovikin, sabon kwamandan dakarun Rasha da ke jagorantar yaki a Ukraine?

An wallafa

Sanarwar da Rasha ta yi na nada sabon kwamandan dakarunta da zai jagoranci yaki a Ukraine, wadda ba a saba gani ba, ta nuna karara cewa Moscow na yin duk abin da ya kamata wajen ganin ta ci gaba a yakin.

Ma'aikatar tsaron Rasha ta bayyana nada Janar Sergey Surovikin a matsayin babban kwamandan dakarun hadin gwiwa da ke aiki na musamman a wasu yankunan Ukraine - wanda mataki ne na yaki da Kremlin ta kaddamar a Ukraine.

Matakin na zuwa ne bayan da dakarun Ukraine sun samu nasarar kai jerin hare-hare kan sojojin Rasha da kuma tilasta wa sojojin ja da baya daga yankunan da Moscow ta ayyana a matsayin yankunanta.

Shiga tsakani a Syria

An haifi Surovikin ne a garin Siberian Novosibirsk, yana kuma da shekaru 55.

An fafata da shi a rikice-rikicen yankin Tajikistan da Chechnya na shekarun 1990, da kuma a baya-bayan nan a Syria, inda Moscow ta shiga tsakani a gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad a 2015.

A watan Yuli, ma'aikatar tsaron Rasha ta ruwaito cewa Surovikin ya jagoranci dakarun kudancin kasar a Ukraine.

Masu fafutukar kare hakkin dan adam sun nuna damuwa kan nadin janar din, ganin cewa ya fuskanci zarge-zargen take yancin dan adam a Chechnya da Syria.

Wani makusancin shugaba Putin da kuma ya kasance jagoran Chenchen, Ramzan Kadyrov da kuma wanda ya kirkiro da kungiyar sojojin haya ta Wagner, Yevgeny Prigozhin dukkansu sun goyo bayan nadin janar din sojan.

Dukkansu sun yi kira ga dakarun Rasha da su kara kaimi sosai a Ukraine, duk da zarge-zargen aikata laifukan yaki kan fararen hula da ake yi wa Rasha.

An fara ganin Sergei Surovikin a kafofin yada labarai a 1991 lokacin da aka so yin juyin mulki kan jagoran mulkin soviet Mikhail Gorbachev.

Surovkin, da ya kasance kaftin din dakarun soji a lokacin, ya shiga aikin soji kan fararen hula da suka yi zanga-zanga a tsakiyar Moscow.

Masu zanga-zangar sun toshe hanyoyi da dama da motocin sojojin za su bi, inda kuma yi ta jifa duwatsu da kolabe.

Surovkin ya bayar da umurnin ci gaba da fafatawa, inda aka kashe mutum uku cikin masu zanga-zangar.

Badakala

An kama Surovkin, inda ya shafe watanni bakwai a tsare yana jiran shari'a, sai dai, daga bisani an soke dukkan tuhuma da ake masa da cewa yana bin doka.

A shekarar 1995, an zarge shi da sayar da bindiga. Wata kotun soji a Moscow ta same shi da laifin, inda ta yanke masa hukuncin daurin shekara daya. Daga baya an cire tuhumar cikin takardunsa.

Sergei Surovikin ya kammala karatu a makarantar sojoji a 2002. Bai jima ba, ya zama kwamanda a birnin Yekaterinbrug, inda shekara biyu baya, ya sake shiga cikin wata badakala lokacin wani abokin aikinsa ya harbe kansa a kusa da ofishinsa.

A 2004, an nada Surovikin a matsayin wata dakarun soja a Chechnya, inda a lokacin Rasha ke gwagwarmayar samun nasara kan wasu mayaka a Moscow.

An sha zargin Surovikin so da dama da laifin tayar da tarzoma kan fararen hula.

Shaidu sun ruwaito cewa wata bataliya karkashin ikon Surovikin ta kai wani samame a wani yanki, inda aka ruguza gidajen fararen hula da dama.

A cewar wadannan rahotannin, gomman maza ne aka musgunawa a wata makaranta, inda aka lakada musu duka da kuma sanya su kwanciya a kasa cikin ruwan sama. Sai dai, Surovikin ya musanta zarge-zargen.

A shekarar 2017, lokacin da Rasha ke taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa dakarun gwamnatin Syria wajen murkushe 'yan adawa a fadin kasar, Sergei Surovikin, ya zama kwamandan dakarun sojin sama na Rasha a Syria. Bai taba aiki da rundunar sojin sama ba sai a wannan shekarar.

A watan Nuwmaban 2017, an nada Surovikin babban kwamandan sojojin sama na Rasha - wani nadi na farko ga wani mutum da ba shi da kwarewa sosai a rundunar soji.

Zargin take 'yancin dan adam

An zargi dakarun soji karkashin jagorancin Surovikin a Syria da laifin take hakkin dan adam, wanda ya kunshi amfani da makamai masu guba da kuma tayar da bama-bamai kan asibitoci.

Wani rahoton kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch na 2020, ya ayyana sunan Surovikin hada da wasu sojojin Rasha da kwamandojin Syria a matsayin wadanda za a tuhuma da laifin take 'yancin dan adam a yankin Idlib daga 2019 zuwa 2020.

Kungiyar ta HRW ta bayyana cewa dakarun Rasha da na Syria sun harba makamai tare da ruguza yankuna.

Wani bincike da jaridar New York Times ta yi a 2019 shi ma ya gano irin wadannan zarge-zarge, sai dai, Moscow ta sha musanta zargin.

An karrama Sergie Surovikin a matsayin zakakurin Rasha, wanda ya kasance babban lambar girma na kasar, sakamakon aike shi zuwa Syria domin yin aiki.

Ba a dai bayyana sunan wanda zai gaje shi ba a hukumance, sai dai, kafafen yada labarai a Rasha sun ruwaito sunan janar Alexander Dvornikov - wanda ya kasance janar da ya jagoranci yakin Chechen na biyu wadda kuma kwamandan dakarun Rasha ne a Syria.