Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bernardo Silva na son barin City, ko Salah zai tafi Saudiyya?
Akwai ƙwarin guiwa a Saudiyya cewa ɗanwasan gaba na Liverpool da Masar Mohamed Salah, mai shekara 32, zai amince ya koma taka leda a gasar Saudi Pro League idan har yarjejeniyarsa ta kawo ƙarshe. (Telegraph - subscription required)
Manchester United na nace kan ɗanwasan gaba na Ipswich mai shekara 22 Liam Delap, wanda farashinsa ya kai fam miliyan 40. (Mail - subscription required)
Newcastle na ci gaba da farautar golan Burnley mai shekara 22 James Trafford. (Sky Sports)
Brighton ta ce duk mai son ƴanwasanta Joao Pedro na Brazil da Carlos Baleba na Kamaru sai ya ware fam miliyan 100 domin daƙile buƙatar Liverpool da Newcastle da kuma Chelsea. (Talksport)
Ɗanwasan tsakiya na Portugal Bernardo Silva, mai shekara 30, yana son barin Manchester City a wannan bazara. (Football Insider)
Arsenal da Newcastle da Chelsea da Manchester United na hamayya kan ɗanwasan gaba na Serbia Dusan Vlahovic, wanda zai iya barin Juventus a bazara. (Gazzetta dello Sport- in Italian)
Newcastle na shirin ɗauko ɗanwasan tsakiya na Ingila mai shekara 22 Harvey Elliott daga Liverpool. (Teamtalk)
Chelsea na nazarin ware fam miliyan 33 domin ɗauko ɗanwasan gaba na Villarreal da Faransa Thierno Barry mai shekara 22 (Fichajes - in Spanish)
Arsenal da Newcastle da Nottingham Forest rubibin ɗanwasan baya na Roma da Ivory Coast Evan Ndicka. (Caught Offside)
Ana sa ran kocin Crystal Palace Oliver Glasner zai koma horar da RB Leipzig a kaka mai zuwa bayan wakilansa sun gana da ƙungiyar ta Jamus. (Sky Germany)