Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
City na son Saliba, Barca ta ce Pedri ba na sayarwa ba ne
Bournemouth na son fam miliyan 45 kan ɗanwasan Serbia Milos Kerkez, mai shekara 21, wanda Liverpool ta nuna tana so. (The Times - subscription required),
Manchester City za ta yi ƙoƙarin sayen ɗanwasan baya na Arsenal da Faransa William Saliba a wannan bazara, duk da ɗanwasan mai shekara 24 na cikin waɗanda Real Madrid ke farauta. (Defensa Central - in Spanish)
Ɗanwasan tsakiya na AC Milan da Netherlands Tijjani Reijnders, mai shekara 26, na cikin waɗanda Manchester City ke farauta. (Teamtalk)
Babu tabbas kan rahotannin da ke cewa ɗanwasan Portugal mai shekara 40 Cristiano Ronaldo, wanda kwangilar shi za ta kawo karshe a Al Nassr ta Saudiyya a wannan barazana zai koma Inter Milan. (Tuttosport - in Italian)
Arsenal na tunani kan ɗanwasan Eintracht Frankfurt da Faransa Hugo Ekitike, mai shekara 22, a matsayin zaɓi idan ta rasa ɗanwasan Newcastle da Sweden Isak, mai shekara 25. (Daily Mirror)
Ana sa ran Chelsea za ta saye sabon gola a wannan baraza. Kocin ƙungiyar Enzo Maresca zai ba golan Serbia Djordje Petrovic, da ya tafi Strasbourg a matsayin aro dama . (Telegraph - subscription required)
Arsenal da ɗanwasan Ingila Bukayo Saka za su fara tattaunawa kan makomarsa yayin sabon daraktan wasanni na Arsenal Andrea Berta ke son ɗanwasan mai shekara 24 ya sanya hannu kan doguwar yarjejeniya. (Fabrizio Romano)
Barcelona ta ce ɗanwasanta na tsakiya Pedri ba na sayarwa ba ne bayan rahotannin da ke alakanta shi da Manchester City, domin maye gurbin Kevin de Bruyne. (Marca - in Spanish)