Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Guardiola: Ba zan horar da ƙungiya ba bayan Man City
Pep Guardiola ya ce bayan ya kammala horar da Manchester City, sai dai ya ja ragamar tawagar wata kasar.
Tsohon kociyan Barcelona da Bayern Munich ya lashe kofi 15 tun bayan da ya karɓi aikin kociyan ƙungiyar Etihad a 2016.
Mai shekara 53 an yi masa tayin horar da tawagar Ingila, amma sai ya zaɓi tsawaita ƙwantiraginsa a Etihad, wanda zai karkare a karshen kakar 2027.
''Ba zan sake kociyan wata ƙungiyar ba,'' in ji Guardiola.
''Abinda nake fata da zarar na kammala aiki da City, zan koma jan ragamar wata tawagar.
Sai dai Guardiola ya ci wasa ɗaya tun bayan da ya sabunta yarjejeniya a Etihad - haka kuma ya doke Nottingham Forest, bayan wasa bakwai a jere ba tare da nasara ba.
Ya fara cin karo da cikas tun bayan da City ta doke Southampton 1-0 a Premier League ranar 26 ga watan Oktoba.
Haka kuma City ta je ta tashi 2-2 da Crystal Palace a wasan mako na 15 a babbar gasar tamaula ta Ingila ranar 7 ga watan Disamba.
City za ta je Juventus a Champions League ranar Laraba daga nan ta karɓi bakuncin Manchester United ranar Lahadi a Premier League.