Newcastle ta ɗauki Osula daga Sheffield United

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Newcastle United ta ɗauki ɗan wasan Denmark ajin 'yan kasa da shekara 21 William Osula daga Sheffield United.

Rahotanni sun ce ɗan wasan gaban ya koma Magpies ne kan kuɗi fan miliyan 15, inda ya ci kwallo uku a wasa 31 da ya bugawa Blades.

Dan wasan da ke buga wa tawagar Denmark ta 'yan ƙasa da shekara 21, ya buga wasa 21 a Premier ga kungiyar Chris Wilder gabanin su faɗa gasar Championship.

"Babbar ƙungiya ce, mai cike da tarihi, ina matuƙar farin ciki da samun wannan damar komawa Newcastle United." in ji Osula.

"Babbar dama ce, kuma ina jin cewa Newcastle United na nema na, na yi maza na ce zan yi amfani da damata."

Kocin Newcastle Eddie Howe ya ce sun dade suna bibiyar ɗan wasan Osula sama da shekara uku, tun bayan hankalinsu da mataimakinsa ya yi masa Jason Tindall, wanda ya dade a Bramall Lane a 2021.

"Dan wasa ne da na sani tun da daɗewa tun lokacin Jason Tindall a Sheffield United," in ji koci Howe.

"Mun dade muna bibiyarsa sama da shekara uku, kuma yana birgemu. Yana da duk abin da ake nema da zai iya zama baban ɗan wasan gaba nan da wani ɗan lokaci."

Osula shi ne ɗan wasa na shida da Newcastle ta siya a bana, bayan zuwan Miodrag Pivas, Odysseas Vlachodimos, John Ruddy, Lloyd Kelly da kuma Lewis Hall.