Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wa zai maye gurbin Rodri a Man City?
Ɗan wasan Manchester City, Rodri ya ji rauni ranar Lahadi a karawar da suka tashi 2-2 da Arsenal a Premier League.
Har yanzu ba a fayyace girman raunin ba, balle a tabbatar da kwanakin da zai yi jinya da ranar da zai koma tamaula, amma wasu na cewar zai ɗauki lokaci mai tsawo.
Pep Guardiola bai taɓa boyewa ba cewar da wuya a samu wanda zai maye gurbin Rodri a Manchester City daga gurbin masu buga tsakiya.
Kalvin Philips ana ganin zai iya buga gurbin Rodri, to amma Guardiola na hangen yana da sauran gogewa, shi ya sa ya bayar da aronsa ga Ipswich kuma sai Janairu zai koma Etihad.
Wasu na ganin watakila Guardiola ya sauya tsarin yadda zai ke fara wasa ta yadda zai ke samun sauki wajen fuskantar ƙungiyoyi ba tare da an yi masa illa ba.
Tsohon ɗan wasan Chelsea, Matea Kovacic zai iya buga gurbin Rodri, ba shi kaɗai ne zaɓi ba a City.
John Stone kan buga tsakiya amma baya hawa sama sosai, domin yana aikin mai tsaron baya ne, wasu lokutan yana yi daga gefen hagu, kenan ana iya saka shi a gurbin mai wasa daga tsakiya.
Ilkay Gundogan ya buga gurbin da Rodri ke yi tun kafin ya bar Etihad zuwa Barcelona a 2023, wanda yanzu ya sake komawa City a bana.
Haka kuma City tana amfani da Bernardo Silva ga kuma Kevin de Bruyne, wanda ke jinya.
Akwai kuma matashi mai shekara 19, Rico Lewis wanda Guardiola ya ce zaɓi ne a wajen shi, wanda ya kware a buga gurbi da yawa.
Idan har Rodri ya daɗe yana jinya, hakika zai kawo koma baya a City a bana, amma dai Guardiola ya kwa da sanin ya zama wajibi ya ɗauki mataki tun kan dare ya yi.
City wadda take ta farko a teburin Premier za ta kara da Watford ranar Talata a League Cup a Etihad, sannan ta je Newcastle a Premier League ranar Asabar.