Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan wasan Brazil da za su buga mata Gasar Kofin Duniya a Qatar
Tawagar kwallon kafa ta Brazil ta sanar da 'yan wasan da za su buga mata gasar kofin duniya a Qatar da za a fara wasannin ranar 20 ga watan Nuwamba.
Brazil tana rukuni na bakwai da ya hada da Serbia da Switzerland da kuma Kamaru, za ta fara wasan farko ranar 24 ga watan Nuwamba da Serbia.
Brazil ta lashe kofin duniya biyar, kuma na karshe da ta dauka shi ne a 2002, sai dai an yi waje da ita a Quarter finals a hannun Belgium da ci 2-1 a 2018 a Rasha.
Brazil ta gayyaci 'yan wasa 12 da ke buga gasar Premier League har da golan Liverpool, Alisson da na Manchester City, Ederson wadanda za su tsare mata raga.
An kira mai tsaron bayan Chelsea, Thiago Silva da mai buga wasan tsakiya a Manchester United, Casemiro da Fred da dan wasan Newcastle, Bruno Guimaraes da na Liverpool, Fabinho da Lucas Paqueta na West Ham United.
Haka kuma Brazil ta gayyaci Dani Alves mai shekara 39 tsohon dan wasan Barcelona, wanda yanzu ke tsaron baya daga hagu a Pumas UNAM ta Mexico.
Cikin masu cin kwallaye da ta gayyata har da dan kwallon Manchester United, Anthony da na Tottenham, Richarlison da fitatcen dan wasa Neymar mai taka leda a Paris St-Germain.
Tawagar ta kara kiran Gabriel Jesus mai taka leda a Arsenal, wanda bai buga mata wasannin sada zumunta a cikin watan Satumba ba.
To sai dai ba ta gayyaci dan wasan Liverpool, Roberto Ferminho ba, wanda ya ci kwallo shida a wasa 12 a Premier League a kakar nan.
Rabon da ya buga wa Brazil tamaula tun wasan da Argentina ta lashe Copa America, amma ta kira 'yan wasan Real Madrid biyu Rodrygo da kuma Vinicius Jr. da dan kwallon Barcelona, Raphinha.
Haka kuma dan wasan Flamengo, Pedto wanda ya yi wa Brazil wasa biyu yana cikin tawagar, mai shekara 25 ya yi murnar jin wannan labari, har da yin baiko da budurwarsa.
Tawagar Brazil da za su buga mata gasar kofin duniya:
Masu tsaron raga Alisson (Liverpool), Ederson (Manchester City), Weverton (Palmeiras)
Masu tsaron baya: Dani Alves (UNAM), Danilo (Juventus), Alex Sandro (Juventus), Alex Telles (Sevilla), Bremer (Juventus), Eder Militao (Real Madrid), Marquinhos (PSG), Thiago Silva (Chelsea)
Masu buga tsakiya: Casemiro (Manchester United), Everton Ribeiro (Flamengo), Bruno Guimaraes (Newcastle), Fabinho (Liverpool), Fred (Manchester United), Lucas Paqueta (West Ham)
Masu cin kwallaye Antony (Manchester United), Gabriel Jesus (Arsenal), Gabriel Martinelli (Arsenal), Neymar (PSG), Pedro (Flamengo), Raphinha (Barcelona), Rodrygo (Real Madrid), Richarlison (Tottenham), Vinicius Jr (Real Madrid).