Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da kuke bukatar sani kan cutar Marburg da matakan kariya
Wasu mutum biyu a Ghana sun mutu bayan kamuwa da cutar Marburg - sannan an killace 98 - inda ake fargabar barkewar wannan cuta mai saurin yaduwa.
Alamomin cutar dai sun hada da tari da ciwon gabobi da gudawa da amai, sannan a yawan lokuta kuma har da rashin jini a jiki.
Mece ce cutar Marburg?
A cewar Majalisar Dinkin Duniya, cutar ta Marburg da ke kama da cutar nan mai saurin kisa ta Ebola, an fara gano ta ne bayan mutum 31 sun kamu da ita, inda bakwai suka mutu a can baya a shekarun 1967 a Marburg da Frankfurt da ke Jamus da kuma a Belgrade a kasar Serbia.
An fara gano cutar ne kan wasu birrai da aka shiga da su daga Uganda.
Sai dai ana kuma danganta cutar da wasu dabbobi tun a wancan lokaci.
Sannan a tsakanin mutane, cutar na yaduwa tsakanin mutanen da suka shafe tsawon lokaci a cikin kogo da ma'adanan da jemagu suka cika.
Wannan ne karon farko da cutar ta bulla a Ghana - sai dai wasu kasashen Afirka da dama sun samu barkewarta, wanda ya hada da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo da Kenya da Afirka ta Kudu da Uganda da kuma Zimbabwe.
Barkewar cutar a kasar Angola a 2005, ya hallaka mutum sama da 300.
Amma a Nahiyar Turai, mutum daya ne kawai ya mutu a shekara 40 - sannan mutum daya a Amurka, bayan dawowa daga balaguro zuwa wani kogo a Uganda.
Jerin Barkewar Cutar da aka samu a Duniya
2017, Uganda: mutum 3 suka kamu, sannan uku kuma suka mutu 2012, Uganda: mutum 15 suka kamu, 4 suka mutu. 2005, Angola: mutum 374 suka kamu, 329 suka mutu.
1998-2000, DR Congo: 154 suka kamu, 128 suka mutu. 1967, Jamus: mutum 29 suka kamu, 7 suka mutu.
Mene ne alamomin cutar?
Alamomin cutar dai na farawa ne da Zazzabin mura tsanain ciwon kai ciwon gabobi.
Sannan bayan kwana uku, cutar tana biyowa da Gudawa mai ruwa-ruwa ciwon ciki tashin zuciya da Amai.
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta ce marasa lafiya a wannan lokaci na nuna siffofi kamar idanu masu zurfi, fuskokin da ba a bayyana su ba da kuma matsananciyar damuwa.
Yawancin mutane kan kuma fama da zubar jini daga wasu sassan jikinsu, inda ta kan kai har mutuwa bayan kwana takwas da kamuwa da ita, saboda yawan zubar jini da kuma kidimewa.
Har ila yau, WHO ta ce a alkaluma da aka tattara, a yawan lokuta cutar ta kashe wadanda suka kamu da ita, sai dai kwayoyinta masu tsanani sun kashe zuwa kashi 88 cikin 100.
Ta yaya ake yada cutar?
Ana danganta wani jemage mai suna rousette da ke kasar Masar a matsayin wacce ke dauke da cutar. Ana kuma samunta a jikin wasu birrai da kuma Aladu a Afirka.
A jikin bil adama kuwa, cutar na yaduwa ne ta hanyar hada jiki da kuma wurin kwanciya daya da wadanda suka kamu da ita.
A wani lokaci kuma, ko da mutum ya warke daga cutar, jininsa kan sa wasu su kamu da ita na tsawon watanni bayan hakan.
Ta ya ake maganceta?
Ya zuwa yanzu, babu rigakafi ko kuma maganin cutar. Sai dai WHO ta ce ana kokarin samar da nau'ikan samfuran jini, da magunguna da kuma rigakafinta.
Likitoci sun ce ana iya rage alamun bayyanar cutar ta hanyar bai wa marasa lafiya a asibiti ruwa mai yawa da kuma maye gurbin jinin da ya ɓaci.
Ta yaya ake taƙaita yaduwarta?
Gavi, da ke aiki da kungiyar kasa da kasa da ke hankoron ganin mutane sun sami rigakafi, ya ce mutane a Afirka su guji ci ko mu'amala da naman daji.
Hukumar Lafiya ta Duniya, ta ce mutane su kuma guji yin mu'amala da Aladu a yankunan da aka samu barkewar cutar.
Har ila yau, an kuma shawarci mutanen da ke dauke da cutar su yi amfani da kwaroron roba na shekara daya bayan fara ganin alamomin cutar ko bayan gwaji ya tabbatar da cewa basa dauke da ita.
An kuma bukaci mutane da ke binne gawa da ta mutu daga cutar da su guji taba gawar.