Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An tabbatar da ɓullar cutar Marburg a Ghana
Ƙasar Ghana ta tabbatar da samun mutum biyu da suka kamu da cutar Marburg, mai saurin kisa da yaɗuwa a wani gida guda.
Mahukunta sun ce duka majinyatan biyu sun mutu kwanan baya a asibiti a yankin kudancin Ashanti.
A farkon wannan watan ne gwajin da aka yi wa samfurin jininsu ya nuna suna dauke da cutar, sannan daga bisani wani dakin gwajin lafiya a Senegal ya tabbatar da sakamakon.
Jami'an kiwon lafiya na kasar sun ce yanzu haka an killace mutane 98 da ake zargin sun kamu da cutar.
Har yanzu babu maganin cutar Marburg, amma likitoci sun ce shan ruwa mai yawa da kuma magance takamaiman alamun cutar na inganta damar rayuwa ga majiyyaci.
Ana ɗaukar cutar ne daga jemagu da ƴaƴan itace, sannan kuma ɓeraye ma na yaɗa ta a tsakanin mutane.
Cutar na da zafi mai tsanani, sau da yawa tana da saurin yin kisa, kuma tana da alamomi da suka hada da ciwon kai, da zazzabi, da ciwon tsoka, da zubar da jini.
Jami’ai na gargadin mutane da su nisanta kansu daga shiga kogo, ko kwazazzabo ko faƙo da duk wasu ramuka da ka iya tara ƙwari, sannan a riƙa dafa nama ƙwarai-ƙwarai kafin a kai baka.
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce akwai cutar dama a Afrika, kamar kasashen Angola da Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da Kenya da Afirka ta Kudu da Uganda.
Barkewar Marburg ta farko ta kasance a Jamus a cikin 1967 inda mutane bakwai suka mutu.
Cutar ta kashe fiye da mutane 200 a Angola a shekarar 2005, lokaci mafi muni da ta bayyana.