‘Burina Najeriya ta zama cikin shiri kafin aukuwar duk wata annoba’
‘Burina Najeriya ta zama cikin shiri kafin aukuwar duk wata annoba’
An wallafa
Sabuwar shugabar hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya (NEMA) ta ce burinta shi ne ta zauna cikin kyakkyawan shiri don tunkarar duk wata annoba da ka iya aukuwa a faɗin ƙasar a kowanne lokaci.
Zubaida Umar ta ce kamata ya yi a ce dukkan jihohin Najeriya su kafa hukumomin ba da agajin gaggawa nasu na kansu, don tunkarar annoba a matakin jiharsu kafin zuwan hukumomin ƙasa da na ƙetare.
Ta ce kamata ya yi a ce abin Allah ya kiyaye, idan an samu wani iftila’i kamar na girgizar ƙasa, Nema tana cikin shirin da za ta iya tattaro ‘yan sanda da ma’aikatan agaji da sauransu cikin ɗan lokaci don kai ɗauki cikin gaggawa.
Ta ce zama cikin shiri shi zai sa a rage asarar rayuka.



