'An yi ta cewa mu jefa ɗanmu a kogi zai tafi ya bi ƴan'uwansa iskokai'

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
'An yi ta cewa mu jefa ɗanmu a kogi zai tafi ya bi ƴan'uwansa iskokai'
An wallafa

Wani magidanci a jihar Nasarawa, ya ce masu magani sun yi ta ruɗar sa cewa ɗansu Hamza, irin yaran nan ne da aljanu ke musanyawa kuma idan suka kai shi kogi, zai tafi ya bi ƴan'uwansa iskokai.

Ya ce ɗan nasa, wanda yanzu ya kai shekara 15, ya gamu da irin larurorin nan ne masu wuyar sha'ani tun a lokacin naƙudar haihuwarsa.

Mallam Abdullahi Amwe ya ce likitoci sun ce ba a cika warkewa daga cutar shanyewar ƙwaƙwalwa (cerabral palsy) da Hamza ke fama da ita ba.

A cewarsa, sun kwashe tsawon shekaru suna neman magani kama daga asibitoci har zuwa wurin masu maganin gargajiya ba tare da sun dace ba.

Ya ce wasu masu maganin gargajiya sun yi ta nuna musu cewa ba rashin lafiya ke damun ɗansa Hamza ba, ɗan ruwa ne kawai aljanu suka musanya musu.

Hausawa suna da wani tsohon camfi na cewa aljanu suna sace jarirai sababbin haihuwa, su musanya da wani aljani da ake kira 'ɗan ruwa' wanda zai yi ta wahalar da iyayen, kuma a ƙarshe ba a ƙarewa lafiya ba, har sai an kai shi bakin kogi, an yar domin ya bi ƴan'uwansa.

Shi dai mahaifin Hamza wanda matarsa kuma ke fama da cutar ƙoda, ya ce irin waɗannan camfe-camfe sun sa iyaye da yawa sun tozarta amanar ƴaƴan da Allah ya ba su, ɗauke da larurori masu wuyar fahimta kamar shanyewar ƙwaƙwalwa.

Ya kuma ce ya koyi yadda zai ja ɗansa a jiki, ya ba shi kulawar da ta dace, kuma har ma wasu iyayen suna kiransa don neman shawarwari game da nasu ƴaƴan masu larura irin ta Hamza.