Kwatancin ƙwazon Mo Salah da sauran gwarazan ƴanwasan gaban Premier

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Andy Cryer
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Senior Journalist
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 3
Kusan duk mako, Mohamed Salah sai ya nuna bajinta.
Ɗan wasan gaban Liverpool ya zura ƙwallo biyu a wasan da ƙungiyar ta lallasa Tottenham da ci shida da uku.
Da wannan nasarar ce Salah ya haura ɗan wasan gaban Manchester City a fafutikar neman zama wanda zai fi zura ƙwallo a kakar bana.
Bayan zura ƙwallo 15 a kakar ta bana, Salah ne kuma ke kan gaba wurin taimakawa a zura ƙwallo, inda bayan wasan na ranar Lahadi, yanzu ya taimaka an zura ƙwallo 11 ke nan.
Ɗan wasan na Masar yanzu ya kama hanyar maimaita nasarar da ya samu a shekarar 2022, inda ya zama wanda ya fi zura ƙwallo, sannan ya fi taimakawa a zura ƙwallo.
Duk da cewa ana ta kwan-gaba-kwan-baya a game da makomar ɗan wasan - kwantiraginsa za ta ƙare a bana - har yanzu yana ci gaba da nuna bajinta.
Amma yaya za a kwatanta ɗan wasan mai shekara 32 da sauran zakarun ƴan wasan da suka taka leda a gasar ta Premier League ta Ingila?
Tsohon mai tsaron ragar Newcastle da Man City da Aston Villa, Shay Given ya shaida wa BBC cewa, "Salah ɗan wasa ne na musamman kuma ya iya taka leda.
"Babban labari a game da shi a yanzu shi ne batun makomarsa. Ba na tunanin za su iya barin sa ya tafi."
Makon kafa tarihi
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Salah ya fara kakar bana da ƙafar dama, inda ya zura ƙwallo 12 a wasa 12 da suka gabata.
Yanzu ya zura ƙwallo 18, sannan ya taimaka an zura 15, ke nan yana da hannu a ƙwallo 33, huɗu ke nan a gaba da duk wani ɗan wasa a manyan gasannin turai.
A wasan Liverpool da Tottenham ya kafa tarihi uku.
- Ya zama na farko da ya haura sa hannu a zura ƙwallo, wato zura ƙwallo da taimakawa a zura sama da goma kafin Kirsimeti.
- Na farko da ya taimaka a zura ƙwallo sama da 10 a kaka huɗu a jere.
- Wannan ne kaka ta shida da Salah ya samu wannan nasarar, inda ya doke Wayne Rooney.
Yanzu Salah zai so ya kafa wani tarihin a wannan kakar, inda yanzu ya mayar da hankalinsa kan lashe takalmin zinare na wanda ya fi zura ƙwallaye a kaka huɗu - nasarar da tsohon ɗan wasan Arsenal Thierry Henry ya taɓa yi.
Salah ya zura ƙwallo 18 a duk kakar da ya taka leda a Liverpool.
Saura ƙwallo biyar ya zama ɗan wasa na biyar da ya taɓa zura ƙwallo 20 a kaka biyar.
Ɗan wasan gaban na Liverpool yanzu yana fafatawa ne da Haaland domin lashe takalmin zinare.
Ɗan wasan na Norway ya zura ƙwallo 27 a kakar bara, sannan ya zura ƙwallo 36 a kaka biyu da ta gabata, inda ya zama ɗan wasa na farko tun bayan Harry Kane na Tottenham da ya lashe kambun wanda ya fi zura ƙwallo a kaka biyu a jere.
Shi ma dai Haaland yana so ya lashe kambun a bana, inda yanzu haka shi ma ya zura ƙwallo 10.
A wane mataki Salah yake a cikin gwarazan gasar?
A wane mataki za a sa Salah idan ana maganar gwarazan ƴan wasan gaban gasar Premier?
Yanzu dai babu shakka Salah na cikin gwarazan ƴan wasan Liverpool, inda ya lashe duk wani kofi da ake buƙata a ƙungiyar.
Shi ne na huɗu a cikin waɗanda suka fi zura kwallaye a ƙungiyar, inda yake da ƙwallo 229 a wasa 373, kuma yake buƙatar ƙwallo 12 domin kamo Gordon Hodgson.
Roger Hunt na da ƙwallo 285, Ian Rush na da 346, waɗanda sun masa nisa, amma idan zai iya ci gaba da zura ƙwallo kamar yadda yake yi a yanzu, zai buƙaci wasa 190 kafin ya zarce su.
A ɓangaren gwarazan gasar Premier League, yanzu haka Salah na cikin gwanayen ƴan wasan gasar, inda yake da ƙwallo 172, kuma shi ne na takwas a jerin waɗanda suka fi zura ƙwallo.
Saura ƙwallo 15 Salah ya kamo na huɗu Andrew Cole - wanda zai iya kamowa a ƙarshen kakar bana.
Amma yaya batun taimakawa a zura ƙwallo?
A wasan na ranar Lahadi, Salah ya kamo David Becham wajen taimakawa a zura ƙwallo 80, inda yanzu su biyun suke mataki na 10. Yanzu yana buƙatar taimakawa a zura ƙwallo 34 domin kamo Kevin de Bruyne, wanda shi ne biyu.
Wanda ya fi taimakawa a zura ƙwallo a gasar Premier League shi ne Ryan Giggs, wanda ya taimaka aka zura ƙwallo 162, amma ya fi Salah buga wasa da wasanni 353.
Amma idan aka haɗa zura ƙwallo da taimakawa, Salah na gaba da shi.
Ya sa hannu a zura ƙwallo 252 a wasa 279 a gasar Premier League, inda ya zama na bakwai a jerin waɗanda jimillar zurawa da taimakawa a zura ƙwallo.
Idan ya cigaba da yadda yake a yanzu, Salah zai kamo Alan Shearer a jimillar zurawa da taimakawa a zura, wato guda 324.
Idan ya sabunta kwantiraginsa, me zai hana shi samun nasarar?











