An buɗe kasuwar cinikayyar ƴan ƙwallo ta Ingila daga 1 ga watan Janairu

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

An buɗe kasuwar cinikayyar ƴan ƙwallo ta Ingila daga 1 ga watan Janairu zuwa 3 ga watan Fabrairun 2025.

Za a yi mako huɗu wajen hada-hada tsakanin ƙungiyoyi, domin kara karfinsu, don kammala kakar tamaula ta bana 2024/25 da ƙwarin gwiwa.

Kenan ƙungiyoyin suna da damar saye ko sayar da ƴan wasa ko kuma ɗaukar aro, ya kama idan tana da bukata ko tana fama da masu rauni da sauransu.

A shekarar 1990 aka bayar da shawarar kafa kasuwar cinikin ƴan ƙwallo, amma sai a 2022/03 aka tsarin a Premier League.

Kasuwa kan yi hada-hada sau biyu a shekara. A watan Janairu ake fara kasuwanci da kuma kafin a fara kakar tamaula ta shekarar.

Cinikayyar da ake daga watan Janairu kan bai wa ƙungiyoyi kara karfinsu, domin kammala kakar tamaula cikin nasara.

Wadda ake yi kan fara kaka kuwa, kan bai wa ƙungioyi damar shirin tunkarar kalubalen da za su fuskanta a fannin tamaula a kakar.

An bukaci ƙungiya ta bayyana ƴan wasa 25 da za ta yi amfani da su, kuma takwas daga ciki daga Ingila, waɗanda aka yi wa rigista da hukumar ƙwallon kafar kasar ko ta Wales.

Haka kuma ƙungiyoyin za su iya amfani da matasa masu shekara kasa da 21, waɗanda ba sa daga cikin 25 da za ta bayyana.

Ya zama wajibi matasan su kasance waɗanda aka haifa tun daga 1 ga watan Janairun 2003.

Haka kuma ƙungiya za ta iya mallakar ƴan wasa biyu daga waje, domin su buga mata wasannin aro, waɗanda ba sa buga tamaula a Ingila.

Ƙungiya za ta iya tuntubar wakilin ɗan ƙwallo dan tattaunawa kafin a buɗe kasuwar cinikayya, amma ba damar ƙulla yarjejeniya sai kasuwar ta fara ci.

Daga nan ne ƙungiya take da damar sayen ɗan wasa, idan an kulla ƙwantiragi, bayan cimma matsaya, ko ɗaukar aro da amincewa da biyan ladan wasa da sauransu.

Daga nan ƙungiyar da ta sayi ɗan wasa za ta gabatar da dukkan takardun da ake bukata da yarjejeniyar da suka ƙulla ga hukumar Premier League.

Daga nan ne Premier League za ta yi nazari kan dukkan takardun da aka mika mata da na damar aiki a Birtaniya, idan daga waje ta ɗauki dan ƙwallo.

Abu da yake kawo tsaiko shi ne auna koshin lafiyar ɗan wasa - tun daga yadda jikinsa yake da tabbatar da cewar bai da wata cuta da za ta kawo matsala da sauransu.