Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Haaland ya haura Rooney a cin ƙwallaye a wasa huɗu da fara Premier
Manchester City ta doke Brentford 2-1 a wasan mako na huɗu a Premier League ranar Asabar a Etihad.
Brentford ce ta fara cin ƙwallo a daƙika 23 da fara tamaula ta hannun Yoane Wissa, shi ne na farko da ya zura ƙwallo a ƙankanin lokaci da fara tamaula da mai rike da kofi.
Daga baya ne Erling Haaland ya farke, sannan ya kara na biyu da ya bai wa City lashe dukkan karawa huɗu da fara kakar nan da haɗa maki 12.
Haaland ya buga karawar duk da zaman makoki tun daga tsakiyar makon jiya da suke na mutuwar aminin mahaifinsa da ya mutu a tsakiyar makon jiya.
Kaɗan ya rage Haaland ya kara na uku a raga a wasan, kenan ya kusan zama na biyar da ya ci ƙwallo uku rigis a wasa uku a jere tun bayan bajintar 1946.
Haaland ya ci Ipswich ƙwallo uku rigis ranar 24 ga watan Satumba da kara cin West Ham uku rigis ranar 31 ga watan Satumba, kafin nan ya zura daya a ragar Chelsea.
Kenan yana da ƙwallo tara a raga a wasa huɗu da fara kakar nan, ya haura Rooney mai takwas a karawa hudu da fara kakar 2011/12.
Haaland ya ci ƙwallo 99 a City a wasa 109, kenan yana zura ƙwallo a raga fiye da daya kenan.
Manchester City, wadda za ta yi wasa uku a gida, za ta karɓi bakuncin Inter a Champions League ranar Laraba 18 ga watan Satumba.
Haka kuma City za ta karɓi bakuncin Arsenal a wasan mako na biyar a Premier League ranar Lahadi 22 ga watan Satumba a Etihad.