Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lille da Real za su kara a karon farko a Champions League
Lille za ta kara da Real Madrid a Champions League ranar Laraba a filin wasa da ake kira Pierre-Mauroy a Faransa.
Wannan shi ne karon farko da za su fuskanci juna a tsakaninsu a babbar gasar zakarun Turai a tarihi.
Real Madrid na fatan cin wasa na biyu a bana, bayan doke Stuttgard a Santiago Bernabeu, kuma Real tana daga 15 da suka haɗa maki uku a karawar farko.
Ita kuwa Lille ta Faransa na fatan samun maki uku a kan Real Madrid, bayan da Sporting ta doke ta 2-0 a karawar farko a gasar a bana.
Kawo yanzu wasa ɗaya Lille ta yi rashin nasara daga biyar da ta fafata a kakar nan, wadda ta yi nasara uku da canjaras ɗaya.
Jonathan David shi ne kan gaba a yawan ci wa Lille ƙwallaye a raga mai bakwai da kuma Edon Zhegrova mai shida.
Tuni kociyan Real Madrid ya bayyana ƴan wasan da ya je da su Lille, domin buga Champions League, wadda take rike da kofin kuma mai 15 jimilla.
Ƴan wasan Real Madrid:
Masu tsaron raga: Lunin, Fran González da kuma Sergio Mestre.
Masu tsare baya: Carvajal, Militão, Lucas V., Vallajo, Fran García, Rüdiger, Mendy da kuma Jacobo.
Masu buga tsakiya: Bellingham, Camavinga, Valverde, Modrić, Tchouameni da kuma Arda Güler.
Masu cin ƙwallaye: Vini Jr, Mbappé, Rodrygo da kuma Endrick.