Fatawar Sheikh Jabir Maihula kan abu biyar da ba sa karya azumi
Fatawar Sheikh Jabir Maihula kan abu biyar da ba sa karya azumi
An wallafa
Sheikh Jabir Maihula wanda malamin addinin Musulunci a jihar Sokoto ya lissafa wasu abubuwa guda biyar da jama’a da dama ke tunanin na karya azumi amma ya ce sam ba sa karya azumin.
Ya karanto wasu hujjoji da magabata domin fayyace dalilan nasa na cewa abubuwan ba sa karya azumi.
Da dama dai masu azumin kan bar bakinsu ba tare da yin burushi ba domin tsoron kada su karya azumin nasu.
To sai dai sheikh Jabir ya ce baya ga burushin ma akwai wasu abubuwa da suka jibanci lafiyar dan'Adam da ba sa karya azumin idan aka yi su.



