Dalilin da ya sa muke so a binciki Amurka kan taimaka wa Boko Haram - Ndume

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu ya bukaci gwamnatin Najeriya ta gaggauta gudanar da bincike kan iƙirarin da wani dan majalisar dokokin Amurka ya yi na cewa hukumar USAID da gwamnatin Trump ta rufe ta tallafawa kungiyoyin ta'addanci da suka hada har da Boko Haram a ƙasar.

Ndume ya ce ba batu ba ne da ya kamata gwamnatin Najeriya ta naɗe hannunta, la'akari da girman barnar Boko Haram a jihar Borno.

Ya ce zai gabatar da kudiri kan binciken zargin dan majalisar dokokin na Amurka.

"In an tashi binciken za mu yi tambayoyi, saboda haka zamu bincika domin mu ƴan Najeriya da abun ya shafa ya kamata mu sa ido don a san matakan da za a dauka, saboda ba ƙaramin barna Boko Haram suka yi mana ba," In ji Ndume.

Sanata Ndume ya yi zargin cewa USAID ba ta aiki tare da hukumomin da ya kamata ta yi aiki tare da su a Najeriya, lamarin da ya ke dasa ayar tambaya, "Ba sa bari jami'an tsaronmu su snaya ido kan abubuwan da suke yi ballantana su bada shawara.

Hukumar bada agaji ta Amurka, USAID an kirkire ta a shekarun 1960 domin taimaka wa ayyukan agaji a madadin gwamnatin Amurka a kowanne yanki na duniya.

Tana da ma'aikata dubu 10, wanda kashi biyu bisa uku na aiki a ketare. Tana da cibiyoyi a sama da kasashe 60, sannan tana ayyuka daban-daban a sauran kasashe.

Sai dai galibin ayyukanta wasu kungiyoyin take bai wa kudi su aiwatar, nata shi ne sa ido da tabbatar da cewa an kashe kudaden bisa tsari.

Ayyukanta na da dimbin yawa. Misali, USAID ba tallafin abinci kadai take bayarwa a kasashe masu fama da yunwa ba, tana kuma aiki wajen gane inda za a fuskanci fari, da kuma inda za a bukaci agajin gaggawa na yiwuwar karancin abinci a nan gaba.

Galibin kasafin kudin USAID ana kashe su ne a fannin lafiya, irin su rigakafin Polio a kasashen da cutar ke yaduwa da kuma taimakawa wajen dakile yaduwar cututtuka da ake yiwa kallon annoba.

Sakamakon dakatar da ayyukan na USAID gwamnatin Najeriya ta ce tana duba yiwuwar fara aiki da mutum 28,000, waɗanda a baya ke aiki da hukumar ba da agaji ta Amurka United States Agency for International Development (USAID).

Da yake magana yayin wata hira da gidan talabijin na Channels TV ranar Juma'a, ministan lafiya na Najeriya, Ali Pate, ya ce gwamnatin tarayya na da niyyar gyara ɓangaren kiwon lafiyar ƙasar yayin da Amurkar ke janye tallafin da take bayarwa ta hannun USAID.

Ministan ya ƙara da cewa Najeriya ba ta zuba kuɗaɗe masu yawa ba a ɓangaren lafiyar, yana mai cewa Shugaba Bola Tinubu "a shirye yake wajen sauya alƙiblar tsarin".

Ya ƙara da cewa fiye da kashi 70 na magungunan da ake amfani da su a Najeirya daga waje ake shiga da su ƙasar.