An sauya ranar da Barcelona za ta buga Sifanish Super Cup 2025

Barcelona

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Hukumar ƙwallon kafa ta Sifaniya ta sanar da sauya ranakun da za a kara a Sifanish Super Cup na 2025.

Tun farko an tsara cewar Barcelona za ta buga karawa ta biyu a daf da karshe, yanzu an tsara cewar za ta yi wasan farko da Athletic Club ranar 8 ga watan Janairun 2025.

Kenan Real Madrid ce za ta yi wasa na biyu na daf da karshe a kofin tare da Mallorca ranar 9 ga watan Janairun 2025.

Barcelona ta samu gurbin buga Sifanish Super Cup ne, bayan da ta yi ta biyu a La Liga a bara, Ahletic kuwa ta lashe Copa del Rey a bara.

Ita kuwa Real Madrid ita ce ta ɗauki kofin La Liga na bara, ita kuwa Mallorca ta buga wasan da Athletic ta doke ta a Copa del Rey a kakar da ta wuce.

Barcelona tana matakin farko a kan teburin La Liga na bana da maki 33 da tazarar maki shida tsakani da Real Madrid ta biyu mai kwantan wasa ɗaya.