Xavi ya yaba wa Ten Hag kan yadda Rashford ya koma ganiya

An wallafa

Barcelona da Manchester United za su kara ranar Alhamis a wasan farko a neman gurbin 'yan 16 da za su ci gaba da buga Europa League.

Kungiyoyin sun yi suna a gasar Turai, sai dai wannan ne karon farko da za su fafata a Europa League.

Tuni Xabi ya yi jinjina ga koci, Erik ten Hag kan yadda ya mayar da Marcus Rashford daya daga 'yan kwallon da ke da hadari a wasannin Turai.

An nada Ten Hag kocin Manchester United kan fara kakar bana, bayan da kungiyar ke fuskantar koma baya.

Tsohon kocin Ajax ya fara farfado da United, wadda a kakar nan take ta uku a teburin Premier, za ta kara da Newcastle a wasan karshe a Carabao Cup.

Haka kuma United tana cikin takarar lashe FA Cup tana kuma fatan cin Barcelona domin ci gaba da karawa a Europa League matakin kungiyoyi 16.

Rashford dan kwallon tawagar Ingila ya zura kwallo 13 a raga a wasa 15, tun bayan kammala gasar kofin duniya a Qatar a 2022.

Ba dan wasan da ya ci kwallaye da yawa tu bayan gama wasannin kofin duniya a manyan gasar Turai biyar, fiye da rashford.

Barcelona za ta buga fafatawar ba tare da Sergio Busquets da kuma Ousmane Dembele, wadanda ke jinya.

To sai dai 'yan wasan Manchester uku wato Antony da Anthony Martial da kuma Scott McTominay ba za su buga karawar ba.

Karo na 14 da za a kara tsakanin Barcelona da Manchester United, inda kungiyar Sifaniya ta ci shida da canjaras hudu, yayin da ta Ingila ta yi nasara a uku.

Wasa 13 a baya da aka buga tsakanin Barcelona da Real Madrid:

2018/2019

Champions League

  • Barcelona 3 - 0 Man Utd
  • Man Utd 0 - 1 Barcelona

2010/2011

Champions League

  • Barcelona 3 - 1 Man Utd

2008/2009

Champions League

  • Barcelona 2 - 0 Man Utd

2007/2008

Champions League Tu 29Apr 2008

  • Man Utd 1 - 0 Barcelona
  • Barcelona 0 - 0 Man Utd

1998/1999

Champions League

  • Barcelona 3 - 3 Man Utd
  • Man Utd 3 - 3 Barcelona

1994/1995

Champions League

  • Barcelona 4 - 0 Man Utd
  • Man Utd 2 - 2 Barcelona

1990/1991

Euro Cup Winners Cup

  • Man Utd 2 - 1 Barcelona

1983/1984

Euro Cup Winners Cup

  • Man Utd 3 - 0 Barcelona

Euro Cup Winners Cup

  • Barcelona 2 - 0 Man Utd