Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An dage wasan neman shiga Champions League bayan kashe dan kallo
An dage wasan neman tikitin shiga gasar Zakarun Turai ta Champions League da za a yi ranar Talata tsakanin AEK Athens da Dinamo Zagreb, bayan da aka daba wa wani dan kallo wuka a babban birnin kasar Girka.
Dan kallon wanda dan kasar Girka ne mai shekaru 29, ya mutu bayan artabu tsakanin magoya bayan kungiyoyin kwallon kafa a wajen filin wasa na AEK Agia Sophia da ke yankin arewacin Athens a yammacin ranar Litinin.
‘Yan sanda sun ce an jikkata wasu mutum takwas amma an kama wasu 98.
Hukumar kwallon kafa ta Turai ta Uefa ta haramta wa magoya bayan kungiyoyin zuwa kallon wasan zagaye na uku na neman shiga gasar saboda matsalar tsaro.
Uefa ta ce biyo bayan rikicin da kuma tuntubar hukumomin kasar ya sa aka dage wasan.
Za a ci gaba da karawa ta biyu a Croatia kamar yadda aka tsara ranar Talata 15 ga watan Agusta, inda za a sake shirya wasan da za a yi a birnin Athens na ranar Juma'a, 18 ga watan Agusta ko kuma Asabar 19 ga watan Agusta.
'Yan sandan Girka sun ce rikicin ya fara ne mintuna 90 bayan da Dinamo ta Croatia ta kammala atisayen tunkarar wasan a filin wasa na Nea Philadelphia.
Magoya bayan Dinamo 100 zuwa 120 ne suka hallara a filin wasan, inda suka yi arangama da magoya bayan AEK da suka taru a wurin.