Ƴan Barca da za su kara da Valencia a La Liga

An wallafa

Barcelona za ta karbi bakuncin Valencia a wasan mako na 33 a La Liga da za su fafata ranar Litinin.

Kungiyoyin biyu sun fuskanci juna ranar 16 ga watan Disambar 2023 a gasar, inda suka tashi 1-1, Barca ce ta fara cin kwallo ta hannun Joao Felix daga baya Hugo Guillamon ya farke.

Barcelona wadda za ta buga wasan a Estadi Olímpic Lluís Companys na fatan yin nasara a karawar, domin ta koma ta biyu a teburi.

Real Madrid ce ta dayan teburi da naki 84, sai Girona ta biyu mai maki 71 da kuma Barcelona ta uku da maki 70.

Barcelona, wadda koci Xavi ya amince zai kara jan ragamar kungiyar kaka daya, wadda ke rike da kofin bara, na fatan yin ta biyu a bana domin shiga Spanish Super Cup a badi.

Ana buga Spanish Super Cup tsakanin wadda ta yi ta daya da ta biyu a La Liga da wadanda suka buga karawar karshe a Copa del Rey a kakar.

Wannan shi ne karon farko da Barcelona za ta yi wasa a La Liga tun bayan da Real Madrid ta doke ta a El Clasico a Santiago Bernabeu.

Tuni kociyan Barcelona, Xavi Hernandez ya sanar da ƴan wasan da za su fuskanci Valencia a ranar Litinin a wasan mako na 33 a La Liga.

Ƴan wasan Barcelona

Ter Stegen, ⁠João Cancelo, R. Araujo, I. Martinez, Ferran, Pedri, Lewandowski, Raphinha, Iñaki Peña, João Félix da kuma Christensen.

Sauran sun hada da Fermín, Marcos A., Romeu, Vitor Roque, S. Roberto, Gündoğan, Kounde, Lamine Yamal, M. Casadó. Kochen, Cubarsí ada kuma H. Fort.