Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Amurka ta yi maraba da kafa majalisar mulki a Haiti
Amurka da ƙasashen yankin Caribbean sun yi maraba da kafa majalisar mulkin Hiati mai mutum tara duk da cewa kawo yanzu babu tabbacin irin mutanen da majalisar za ta kunsa da kuma lokacin da zata fara aiki.
Wannan na zuwa ne wata ɗaya Firaiminista Ariel Henry ya sanar da cewa zai yi murabus, yayin da ake ci gaba da samun raoton aikata manyan laifuka a babban birnin ƙasarPort-au-Prince.
Ana dai sa ran sabuwar majalisar mai mutane 9, wadda aka naɗa za ta yi aiki ne domin farfado da zaman lafiya a ƙasar da yaƙi ya ɗaiɗaita.
Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce mutane aƙalla dubu ɗari ɗaya ne suka yi hijira daga babban birnin ƙasar, kuma a gefe guda ƴan siyasa da sauran masu faɗa-aji suna ci gaba da jayayya a kan wanda ya kamaya Ya jagotanci gwamnatin rikon ƙwaryar.
Da alama dai a shawo kan dambarwar siyasar ƙasar, kuma kawo yanzu babu tabbacin ko su wanene sabbin ƴan majalisar mulkin, waɗanda ake sa ran su ne za su mayar da ƙasar kan turbar dimokuradiyya.
Daga cikin ayyukan da wannan majalisa za ta gudanar dai har da nadin shugaban ƙasa da kuma firaiminista.