Lewandowski ba zai buga El Clasico da Real ba a Copa del Rey

An wallafa

Robert Lewandowski ba zai buga wasan farko na daf da karshe a Copa del Rey da Barcelona ta ziyarci Real Madrid ranar Alhamis ba.

Ba a fayyace ranar da zai koma taka leda da, amma kungiyar za ta ci gaba da auna koshin lafiyarsa, don fayyace ranar da ya kamata ya koma buga mata wasanni.

Tsohon dan kwallon Bayern Munich, shine kan gaba a ci wa Barca kwallaye a bana, wanda ya zura 25 a raga a dukkan fafatawa 31, har da 15 a La Liga.

Raunin Lewandowski wani koma baya ne ga kungiyar da Xavi ke jan ragama, bayan da Almeria ta ci Barcelona 1-0 ranar Lahadi a La Liga.

Haka kuma Ousmane Dembele da Pedri na jinya, ba za su buga fafatawar hamayyar ba.

To sai dai Ansu Fati ya murmure yana cikin wadanda Barca ta ziyarci Real Madrid da shi.

Wasa na biyu kenan da aka ci kungiyar Camp Nou a La Liga a kakar nan, wadda ta barar da damar bai wa Real Madrid tazarar maki 10 tsakani.

Haka kuma Barcelona ta ci karo da cikas a bana, bayan da Manchester United ta fitar da ita da cin 4-3 gida da waje a wasan neman shiga Europa League zagayen 'yan 16.

Barcelona za ta fara zuwa Santiago Bernabeu ranar 2 ga watan Maris, domin buga wasan farko na daf da karshe a Copa del Rel na bana.

Daga nan za ta fafata da Valencia da kuma Athletic Bilbao a gasar La Liga, sannan ta karbi bakuncin wasa na biyu a Copa del Rey da Real ranar 19 ga watan Maris a Camp Nou.

Cikin Janairu Barcelona ta ci Real 3-1 ta lashe Sifanish Super Cup a Saudi Arabia, kafin nan Real ce ta fara cin Barca 3-1 a kakar bana a La Liga a 2022.

'Yan wasan da Barca ta je da su Real Madrid:

Ter Stegen, R. Araujo, Sergio, Gavi, Ansu Fati, Ferran, Iñaki Peña, Christensen, Marcos Alonso, Jordi Alba da kuma Kessie.

Sauran sun hada da S. Roberto, F. De Jong, Raphinha, Kounde, Eric, Balde, Pablo Torre, Arnau Tenas, A. Alarcón da kuma Estanis.