Yadda tankokin yaƙin ƙasashen yamma za su sauya yaƙin Ukraine

Tankar yaki

Asalin hoton, EPA

An wallafa

Shin Ukraine za ta iya samun nasarar yaƙin da take yi a wannan mako?

Haƙiƙa wannan lokaci ne na samun ƙwarin gwiwa ga Ukraine, a yayin da ƙawancen ƙasashen yamma suka tabbatar da cewa za su tallafa mata da sabbin tankokin yaƙi na zamani.

A yayin da ƙasashen Jamus da Amurka suka ce za su aika wa Ukraine tankokin yaƙi na zamani, tuni ƙasashen Birtaniya da Poland suma suka alƙawarta tura nasu makaman, yayin da ake sa ran sauran ƙasashen yamma za su biyo baya.

Tuni dai wasu masu sharhi suka bayyana lamarin da cewa abu ne da zai sauya salon yaƙin.

Shin da gaske hakan zai zai iya sauya salon yaƙin?

Ben Barry, babban jami'i a cibiyar tsare-tsaren yaƙi ta ƙasa-da-ƙasa ya shaida wa BBC cewa tankokin za su sauya fasalin yaƙin. To sai dai tsohon jami'in ya yi gargaɗin cewar alƙawuran da ƙasashen yamman suka yi ka iya zama yaudara.

A yaƙin wannan zamani, tankoki suna daga cikin manyan makamai na kai hare-hare kan abokan hamayya domin ƙwace yankuna.

Matuƙar aka yi amfani da su yadda ya kamata, za a samu ƙarfin kai hari, da kariya, za kuma su iya sauya akalar harin abokan adawa.

To sai dai suna buƙatar taimakon makaman roka domin rage ƙarfin abokan adawa tare da sojojin ƙasa waɗanda za su taimaka wajen ƙwace yankunan da ke hannun abokan hamayya.

Tarihi ya nuna cewa tankoki kaɗai ba za su iya yin nasarar yaƙi ba. Domin Kuwa a shekarar 1917 Birtaniya ta yi amfani da ɗaruruwan tankokin yaƙi a yaƙin Cambrai, amma duk da haka ƙarfin hare-haren Jamus sun tilasta lalata mafi yawa daga cikin tankokin, inda daga ƙarshe Jamus ɗin ta yi nasara a kan Birtaniyar.

Ukraine ta faɗa ƙarara cewa tana bukatar makaman ne ba don tsayar da hare-haren Rasha kawai ba, sai don ƙwato yankunanta da ke hannun Rasha, ta hanyar ƙaddamar da jerin hare-hare.

Yadda Ukraine za ta yi amfani da tankokin

Girke tankokin yaƙin a filin daga da Ukraine za ta yi na kusan sama da kilomita 1,000 zai tamaka wa ƙasar samun nasara a yiƙin da take yi.

Domin kutsawa cikin ƙarfin tsaron Rasha, Ukraine na bukatar mayar da hankali wajen kimtsa dakarunta a yankunan da ake fafatawar.

Idan Ukraine ta samu waɗannan tankoki za ta yi ƙaoƙarin yin luguden hare-hare a yankuna daban-daban, kamr yadda ta yi a shekarar da ta gabata a arewaci da kudancin kudancin ƙasar.

Birtaniya ba tankoki kaɗai za ta aika wa Ukraine ba, har da makaman artillery 30 da motocin sulke domin ɗauka tare da kare sojoji.

Amurka ma ta alƙawarta taimaka wa Ukraine ɗin da motocin sulke fiye 100, yayin da Jamus ta alƙawarta bayara da motocin sulken 40 tare da tankokin yaƙi.

Tankoki ne na zamani

Sabbin tankokin yaƙin sun zarta na Rasha sauri, inda suke gudun kilomitoci masu yawan gaske cikin sa'a guda a ƙasa.

Haka kuma tankokin na da nauyin tan 20 fiye da na ƙasar Rasha.

Ƙarin makaman yaƙin za su taimaka wajen inganta ƙarfin tankokin, to sai dai nauyin da tankokin ke da shi zai iya zamar musu ƙalubale wajen tsallaka wasu gadojin ƙasar.

A baya ƙasashen Rasha da Ukraine sun yi ta karya gadoji ta hanyar kai musu hare-haren rokoki.

Ƙalubalen amfani da tankokin

Babban ƙalubalen da Ukraine za ta fuskanta game da waɗannan makamai shi ne gudanarwar yau da kullum, ci gaba da zuba musu man da za su yi amfani da su, da harsasai, da kayan gyaransu.

A yanzu Ukraine za ta fukanci ƙarin wahalhalun samar wa da sabbin tankokin abubuwan da suke buƙata, baya ga wahalar da take sha a yanzu na samar wa kanta abin da tankokinta ke buƙata.

Kuma tankokin da Birtaniya ta alƙawarta bayarwa, harsasan da suke amfani da su da su na matuƙar wahalar samu, domin kuwa sai a Birtaniyan kaɗai ake samun irin harsasan da suke amfani da su.

Mista Barry ya ce ta yiyu Injiniyoyin Ukraine sun san yadda ake yi musu juyen bakin mai.

To sai dai a cewarsa tankokin Amurka na da wahalar sha'ani ta fuskar juye da gyara. Haka kuma suna shan mai na kusan ninki biyu a kan na Jamus.

Tankar yaƙi

Asalin hoton, Getty Images

Idan alƙawarin ƙasashen yamman ya tabbata, hakan zai bunƙasa dakarun Ukraine da fiye da tankokin yaƙi 100, duk da haka bai kai abin da babban kwamandan sojin ƙasar ya buƙata.

A watan Oktoban bara, Janar Valerii Zaluzhnyi ya ce Ukraine na buƙatar ƙarin tankoki 300, da motocin sulke 700, da kuma makaman harba rokoki 500 a shekarar da ta gabata.

Haka kuma horon amfani da makaman na buƙatar lokaci, wataƙila makwanni, in ma ba watanni ba, sannan kuma ba a san zuwa yaushe waɗannan makamai za su isa ga Ukraine ɗin ba.

Ukraine dai ta daɗe tana bayar da mamaki a wannan yaƙi, to sai dai duk da haka tana buƙatar taimakon ƙasashen yamma domin samun galaba a kan dakarun Rasha.