Ƙarairayi biyar da ake yaɗawa kan sauyin yanayi

An wallafa

Bukatar daƙile matsalolin sauyin yanayi ba abu ne da wai ake zuzutawa ba – sai dai a yanzu, a shafukan sada zumunta, labaran boge na tasiri a zuƙatan mutane wajen fahimtar abin da ake nufi da dumamar yanayi.

Yayin da ake taron sauyin yanayi karo na 27 a Masar wato COP27, masu bincike kan sauyin yanayi sun karu a shafukan intanet, hakazalika labaran boge da ake yaɗawa.

Ga wasu kalilan da aka fi yawaita tsokaci a kai.

Masu iƙirari: 'Sauyin yanayi ba gaskiya ba ne'

Wasu mutane da ke da yaƙinin cewa sauyin yanayi ba gaskiya ba ne ko ba ya faruwa na yarda da shaci faɗin mutane a matsayin wata hanyar tabbatar da tunaninsu.

Su na da yardar cewa batun sauyin yanayi wani shiryayen batu ne na sirri da tsiraru a duniya masu karfi faɗa a ji ke yaɗawa.

Wasu kuma na cewa wata hanya ce ta cin kuɗi kawai – ko kokarin daƙile wasu haƙoƙi ko 'yancin mutane. Babu wata hujja da ke iya tabbatar da wannan iƙirari.

Sai dai kaso 99 cikin 100 na kwarraru a fanin kimiya, sun yarda da cewa sauyin yanayi dagaske ne kuma abu ne da ɗan adam ya haddasa shi.

Tun shekara ta 1850, dumamar yanayi a duniya ya karu da maki 1.1 bisa ma’aunin salshiyos, a cewar wani kwamitin kwararru da ke nazarin kan harkokin sauyin yanayi tsakanin kasa da kasa a duniya, IPCC, a Majalisar Dinkin Duniya.

Sakamakon hakan, matsalolin da yanayi ke haifarwa na matukar ƙaruwa, tare da haifar da barazana ga rayuka da lamuran yau da kullum a ko ina a duniya.

"Babu shaka ɗabi’un mutane sun yi tasiri wajen ta’azzara matsalolin yanayi a doron kasa da teku da duniya baki ɗaya", a cewar rahoton IPCC.

"Sauyin yanayi na faruwa a ko ina a koda yaushe: muna bukatar nazartar abin da ke faruwa a wannan shekara domin yarda da hakan", a cewar Dakta Ella Gilbert, kwararriyar masana kimiya daga Burtaniya.

Ikirarin: 'Sauyin yanayi matsalar ƙasashen yamma ne'

Ana danganta matsalolin dumamar yanayi da fitar da sinadaran hayaki ko tiriri irinsu cardon dioxide da ke haɗewa da rana na haifar da yanayi mai zafin gaske.

Manyan ƙasashen duniya masu arziki ake ɗaurawa alhaki a tsawon shekaru na tarihi – irinsu Amurka da Burtaniya da Jamus.

Ga mutane da dama a matalautan kasashe, wannan ne ya sa shawo kan matsalar ke da wahalar gaske ga ƙasashen yamma.

Amma sauyin yanayi ba shi da iyaka kuma tuni illarsa ke sake fitowa filli, misali a Pakistan, inda ake da yaƙinin cewa sauyin yanayi ya taka rawa sosai wajen mummunan ambaliya da suka fuskanta kwanan nan.

Bincike ya kuma nuna cewa kasashe matalauta ne tasirin sauyin yanayi zai fi shafa – saboda wasu dalilai, da kuma rashin karfin shiryawa ko amfani da wasu dabarun tunkarar matsalolin.

"Sauyin yanayi matsalar ce ta duniya", a cewar Dakta Lisa Schipper, kwararriyar mai bincike daga Jami’ar Bonn ta Jamus.

Kasashe mafiya talauci a duniya, ba wai su illar take shafa kai tsaye ba, su ne dai ake yiwa kallon wakilan iya tabbatar da canji".

Wannan shi ne dalilin da ya sa gwanatocinsu ke son ake sauraronsu idan ana tattauna batun sauyin yanayi – ciki harda taron COP27, da batun adalci kan sauyin yanayi zai kasance manyan batutuwan tattaunawa a kai.

Ikirarin: 'Sauyin yanayi na iya zama alheri a garemu'

Ga ƙasashen da ke fama da tsananin sanyi, batun duniya mai dumi na iya kwaɗaitar da su ko jan hankalinsu a karon farko.

Misali, kalaman Shugaba Putin: a shekara ta 2003, yana cewa idan Rasha ta tsinci kanta cikin yanayi na zafi, mutane za su rage kashe kuɗaɗe a fanin sayen kayan sanyi, sannan noman hatsi zai karu – ra'ayin da har yanzu ake yawo da shi a shafukan sada zumunta.

Matsalar ita ce duk wani riba da ake ganin sauyin yanayi zai kawo to na gajeren lokaci ne, domin nan gaba za a fahimci illarsa a faɗin duniya.

IPCC ta kiyasta cewa idan yanayin duniya a mataki matsaƙaici ya kai maki 1.5 bisa ma’aunin salshiyos kafin karshen karni, ana iya tafka asarar dala tiriliyan 54, sannan kuɗaɗe za su kai har dala tiriliyan 69 idan ya kai maki 2.

Makomar za ta bada mamaki: Kasashen Gabas Ta Tsakiya za su ga gonakinsu sun koma tamkar sahara; Yankunan tekun Pacific za su ɓace baki daya su zama teku; kasashen Afirka da dama za su fuskanci fari.

Ko a kasashe masu tsananin sanyi irinsu Rasha, wutar daji – irin wanda ake gani na tashi a yankunan Siberia a 2021 – za ta karu matuƙa, yayinda tsananin zafin ke karuwa da bushewar ko ina.

Iƙirarin: 'Ruwan teku baya ƙaruwa. Igiyar teku ke tunbatsa’

A cewar hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka, NASA, ta shanye kusan kashi 90 cikin 100 na gargadin da ake yi kan sauyin yanayi a shekarun baya-bayanan saboda karuwar sinadarin hayaƙi da take fitarwa.

Sakamakon haka, ana samun narkewar kankarar teku. Sannan ruwa na karuwa yayin da yanayi ke sake ɗumi, hakazalika teku na sake girma sakamakon tsananin sauyin yanayin.

A shafukan sada zumunta, an sha ganin yadda mutane ke daukan abin da wasa suna ganin wani yanayi ne na tunbatsar teku – amma zance na gaskiya abin ya wuce tunani.

Igiyar teku na sasauyawa: suna wakiltar wani canji da ake gani a kullum a kodayaushe.

Amma an kiyasta cewa, a cikin shekaru kusan 100, ruwan teku ya karu da inci 6 zuwa 8. "Wannan ya zarta wanda aka taɓa samu a karni na 20", a cewar Ken Rice, wani farfesa a Jami’ar Edinburgh.

Iƙirari: ‘An makara magance batun sauyin yanayi'

Abu ne mai wahala mutumin bai zai ji wani abu ba kan kanun labaran da ake wallafawa kan sauyin yanayi.

Maganganun da ake yi kan 'gargadin karshe' ko 'ana cikin hadari' na iya tada hankali ko jefa damuwa.

Wannan na iya sa mutum ya soma tunani kawai lokaci ya kure masa – kuma sadadun da ake nunawa na karuwa, akwai tunani duniya ta makara.

Babu zaɓi kan batun – yanayin dai na sauyawa, kuma tasirin hakan abu ne da za a shafe tsawon shekaru aru-aru ana gani.

Amma akwai labari mai daɗi. Godiya ga kwararru a fanin kimiya, an fahimci abubuwan da ake bukata ko matakai domin rage raɗaɗin tasirin ko matsalar da za a iya fuskanta.

Dole kasashe su rage fitar da hayaƙi mai gurbata muhalli, yayinda – a ɓangare guda – ana bijiro da hanyoyin kawar da yanayin da ake ciki.

Wannan shi ne dalilin shirya taro irin na COP27 – dama ce ga ‘yan siyasa su haɗu waje guda su tattauna matakan da ya kamata a ɗauka kan sauyin yanayi.

"Duk wani mataki da za a iya ɗauka domin kawo sauyi abin maraba ne’’, a cewar Dakta Gilbert na Burtaniya.