Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Labarin abokai huɗu da aka yi wa kisan gilla a gidansu a Abuja
Labaran wasu mutum huɗu da aka yi wa kisan gilla kwanan nan a wani gida a Abuja, babban birnin Najeriya, ya mamaye kafafen yaɗa labaran ƙasar.
A yayin da mutane ke ta jimamin yadda wannan abu ya faru, su kuwa ƴan uwa da abokan arzikin wadanda aka kashe ɗin har yanzu suna cikin fargaba da kaɗuwa da ɓacin rai suke, suna roƙon jami'an tsaro su taimaka wajen gano musabbabin mutuwar mutanen.
Wani abokin biyu daga cikin mamatan Fiamarri Machar Zoaka ya fashe da kuka a lokacin da yake bai wa BBC labarin.
Ya ce ɗaya daga cikin mamatan Samson Pankyes Anpe, wanda ake kira da ‘Chopboii’, abokinsa ne fiye da shekara 20.
Yadda Chopboii ya ɓata da kuma cigiyarsa
Di Fi’ammari da Chopboii abokai ne ƙud da ƙud. Ya ce shi da Chopboii sun halarci makaranta ɗaya kuma ma rukuninsu na rawa ɗaya. A wasu lokuta Chopboii kan yi kwanaki a gidansu, kuma yana jiran sa ya je a ranar 25 ga watan Satumban 2022 amma bai je ba.
"Duk lokacin da Sam ke son ya huta, yakan zo gidanmu ya yi kwanaki kuma koyaushe yana magana da iyayensa. Yana yawan magana mahaifiyarsa da 'yan uwansa mata, amma ranar sai wani abu daban ya faru," a cewarsa.
"Sun kira ni suka ce ba su ga Sam ba kuma wayoyinsa a kashe. Na gwada layukansa ba sa shiga. Na yi mamaki saboda ya ce min zai gidana ranar Lahadi amma da na ga ban gan shi ba sai na zaci ya shiga wata sabgar ne.
"Daga baya sai suka faɗa min yana tare da Peter Gwezi Ugbomah (ɗaya daga cikin mutanen), na kira shi shi ma amma lambarsa ba ta shiga.
"Na san Peter kusan shekara 10 shi ma."
Fi’ammari ya ce sai a ranar Talata suka fara fahimtar abin da ke faruwa.
"Muna tsaka da nema, a wannan Talatar budurwar ɗaya daga cikin abokanmu ta faɗa mana cewa ta san wani gida Chopboii ke zuwa a Gwarimpa, mu je mu bincika."
A cewarsa, sukan shafe kwanaki ba su gan shi ba amma sukan gan shi shafukan sada zumunta. "Saboda yana yawan saka waƙoƙinsa da rawa, da su yake tallafa wa iyayensa da matarsa mai ciki."
Fia’mmari ya ce ya kira mutumin da yake ba su bayanai kan sa, shi ne ya ce musu su yi sauri su je Gwarimpa.
"Da na sake kira sai suka ce min na zo Gwarimpa. Lokacin da na je sai jikina ya ba ni cewa ya mutu.
"Yan sanda sun ce mu ko koma baya saboda an killace wurin a matsayin waje da aka aikata laifi. Kwamashinna 'yan sanda na Abuja da kuma tawagar bincike duk sun je wurin.
"Sun ƙyale ni na shiga ne saboda sun ce ni ne mafi kusa da Sam kuma don na tantance gawar tasa."
Ya ƙara da cewa abin da ya gani shi ne mafi muni a rayuwarsa.
"Na ga gawarwaki a ƙasa, na ga jini a ko'ina. Sun rufe gawar Peter ba mu iya gane shi ba ne. Shi kaɗai ne a rumfa yayin da sauran ke cikin ɗaki.
"Sun ce maharan sun farfasa kawunansu sannan suka daddatsa jikinsu.
"Mun ga sun fasa kan Peter, suka karya wuyansa, suka cire kan da yatsunsa, sannan suka rubuta "him" (shi) a jikin bango da jini. Sannan sun rubuta a jikin bango cewa: 'Na faɗa musu kar su yi wasa da ita.
"Sun daddatsa macen yadda ba za a iya gane ta ba, daga aka gane Blessing Udie.2 ce. "Wannan ne abu mafi muni da na taɓa gani a rayuwata."
Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen Abuja ta ce tana zargin aikata kisan kai ne.