Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Shagunana uku ne suka kone a kasuwar Fanteka'
Daya daga cikin masu shaguna a sabuwar kasuwar Fanteka da ibtila'in gobara ya afkawa a baya-bayan nan ya ce shagunansa guda uku ne suka kone kurmus.
Murtala Usman, wanda ya ce yake sana'ar katako da kusoshi da kayan gine-gine ya ce ya yi asarar kimanin naira miliyan 30 zuwa 35 sanadiyyar gobarar da ta tashi cikin dare.
"Yanzu wurin ya zama kamar filin kwallo, babu komai in ban da pol-pol na wuta sai kuma ragowar injinan yanka katako wanda su karafa ne - amma saboda wuta sun lankwashe." in ji dan kasuwar.
A hirarsa da BBC, Murtala Usman ya ce baya ga shi, akwai sauran yaransa na kasuwa da ya yaye da suma suka tafka asarar miliyoyin kudi.
Ya ce akwai kayayyakin da aka sauke musu a kwana uku cikin tirela-tirela kuma a yanzu duka sun yi asarar kayayyakin.
Shi ma Abubakar Alhaji Garba, mai sana'ar katako da kusoshi a kasuwar, ya ce, a bangarensa, ya yi asarar da ta kai ta kusan naira miliyan tara na katakon da yake sayarwa.
Ya ce "na sauke motar dan Taraba guda daya, ina ga ba mu yi cinikin naira dubu dari biyar ba, gobarar ta kone su." A cewar sa, bai yi asara ba ta bangaren kusoshin da yake saidawa.
Dan kasuwar ya ce yana fatan gwamnati za ta kai musu daukin da ya kamata domin taimaka musu wajen sake komawa harkokinsu na kasuwanci.
'Farfadowa daga ibtila'in zai kai ni shekara biyu zuwa uku'
Murtala Usman ya ce duk da cewa farfadowa tana wajen Allah ya ce suna kai kukansu ga gwamnati ta taimaka musu.
A cewar sa, farfadowa daga irin wannan lamari sai sannu a hankali "tun da ba daina kasuwanci za a yi ba don samun abin da za a ci na yau da kullum" inda ya ba da misali da irin ibtila'in da ya taba shafarsu shekaru shida da suka gabata kuma wurin ya gyaru kamar ba a taba yin gobara ba.
Sai dai ya ce gobarar ta yanzu ba ta kai girman wadda ta afku a baya ba.
"Rayuwar sai dai hakuri, don dole a fuskanci kalubale saboda muna fama da abin da ake cewa hannu-baka-hannu-kwarya - sai ka fito ka yi ciniki sannan ka koma ka yi cefane ka jira na gobe ya samu ka dan ajiye." kamar yadda ya ce.
Abin da muka sani kan gobarar ta kasuwar Fanteka
Shugaban kasuwar, Alhaji Suleiman Shehu ya bayyana wa BBC cewa har yanzu ana gudanar da bincike domin kiyasta girman barnar da gobarar ta haifar.
Ya ce kwamitin da suka kafa domin yin wannan aiki yana ci gaba da nazari tare da karbar bayanai daga yan kasuwar da lamarin ya shafa.
Ranar Laraba ne shugaban kasuwar ya ce akalla shaguna 250 ne suka kone kurmus bayan gobarar da ta tashi.
Ya kuma ce ba a zamu asarar rayuka ba amma dukiya ta salwanta.