Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wasu ayyukan da Shugaba Buhari zai ƙaddamar a Legas
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na gudanar da ziyarar aiki ta kwana biyu Jihar Legas da ke kudancin Najeriya.
A lokacin ziyarar, shugaban zai ƙaddamar da wasu ayyuka waɗanda gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu ya aiwatar a jihar da kuma waɗanda wasu kamfanoni suka yi.
Manyan ayyukan da shugaban ƙasar zai ƙaddamar sun haɗa da tashar ruwa ta Lekki da kuma wani kamfanin casar shinkafa da wani titi mai tsawon kilomita 18.75 da kuma wata cibiyar tarihi ta Yarbawa wato John Randle Center.
Sauran sun hada da kamfanin man juyen mota na MRS da ke Apapa da aikin jirgin kasa na Blue Line Rail Project.
Haka kuma ana sa ran shugaban zai shaida sanya hannu kan aikin layin dogo na biyu wanda zai tashi daga Mile 2 zuwa Okokomaiko.
Ayyuka mafi girma da za a ƙaddamar su ne na tasahar ruwan Lekki da kuma aikin jirgin ƙasa na Blue Line.
Aikin tashar ruwan haɗin gwiwa ne tsakanin gwamnati da kuma kamfanoni masu zaman kansu.
Rahotanni sun ce tashar ruwan ta Lekki ita ce mafi girma a nahiyar Afrika.
Sai kuma aikin jirgin ƙasan na Blue Line wanda gwamnatin Legas ta yi shi ne irinsa na farko da wata gwamnatin jiha ta aiwatar.
Gwamnatin jihar dai ta ce ta ƙirƙiro wannan aikin na jirgin ƙasan ne domin rage cunkoson ababen hawa da ya addabi jihar shekaru aru-aru.
Lokutan baya da Shugaba Buhari ya kai ziyara Legas
Lokaci na ƙarshe da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya je Legas shi ne Maris ɗin 2022 inda ya ƙaddamar da kamfanin takin zamani na Dangote tare da kuma duba ayyukan matatar mai ta Dangote da kuma tashar ruwa ta Lekki.
A watan Yunin 2021, Shugaba Buhari ya je Legas inda ya ƙaddamar da sufurin jiragen ƙasa daga Legas zuwa Ibadan.
Haka kuma a 2019, Shugaba Buhari ya je Legas inda ya ƙaddamar da cibiyar kula da mata da yara wadda aka ƙara ingantawa da ke cikin asibitin koyarwa ta Jami'ar Legas.
A 2018 kuma shugaban ya ƙaddamar da ofishin Ecowas da ke iyakar Najeriya da Jamhuriyyar Benin wadda ke a Seme. Gwamna Akinwumi Ambode ne ma ya tarbi Shugaba Buhari a lokacin.
Haka kuma a shekarar, shugaban ya je Legas inda ya ƙaddamar da tashar motocin bas na haya kuma na zamani da ke Ikeja.