An kori Bellingham a wasan da Real ta yi canjaras da Valencia

An wallafa

An kori Jude Bellingham bayan korafin da ya yi bayan an soke ƙwallon da ya jefa a ragar Valencia a gagarumin wasan da aka buga a filin wasan Mestalla.

Vinicius Jr ya zura wa Madrid ƙwallaye biyu a filin wasan da ya fuskanci cin zarafin wariyar launin fata a bara, inda Real ta farfaɗo daga ci 2-0 don ceto maki ɗaya inda wasan ya ƙare ci 2-2.

Bellingham dai ya yi tunanin ya samu nasara a wasan ne a cikin minti shida na ƙarin lokaci a ƙarshen wasan, sai dai alkalin wasa Gil Manzano ya busa tashi kafin ƙwallon ta ƙaraso da'ira ta 18.

Ƴan wasan Real da ma'aikatansu sun kewaye Manzano, kuma Bellingham, wanda ke buga wasansa na farko bayan makonni uku yana jinya, ya karɓi jan kati sakamakon ƙorofin da ya yi wa alƙalin wasan, yanzu yana iya fuskantar dakatarwa na wasanni biyu idan har Real ba ta ɗaukaka ƙara kan katin ba.