'Yan Real da za su kara da Espanyol a La Liga ranar Asabar

Asalin hoton, Real Madrid FC
Real Madrid za ta karbi bakuncin Espanyol ranar Asabar a wasan mako na 25 a gasar La Liga a Santiago Bernabeu.
Ranar 28 ga watan Agustan 2022, Real ta je ta ci Espanyol 3-1 a gasar La Liga ta kakar nan.
Wadanda suka ci wa Real Madrid kwallayen sun hada da Vinicius Junior da ya zura daya a raga da Karim Benzema da ya ci biyu daf da daf kuma daf a tashi.
Ita kuwa Espanyol ta zae kwallo daya ta hannun Joselu a wasan da ta karbi bakunci.
Real Madrid tana mataki na biyu a kan teburin La Liga da maki 53 da tazarar maki tara tsakaninta da Barcelona ta daya mai 62.
Espanyol tana ta 13 a kasan teburin kakar bana mai maki 27.
Tuni kociya, Carlo Ancelotti ya bayyana 'yan wasan da zai suskanci Espanyol ranar Asabar.
'Yan wasan Real Madrid:
Masu tsaron raga: Courtois, Lunin, Luis López.
Masu tsaron baya: Carvajal, E. Militão, Vallejo, Nacho, Odriozola, Lucas V., Rüdiger.
Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde, Tchouameni, D. Ceballos.
Masu cin kwallaye: Hazard, Asensio, Vini Jr., Rodrygo, Mariano, Álvaro.
Wasannin mako na 25 da za a buga a La Liga:
Ranar Juma'a 10 ga watan Maris
- Cadiz da Getafe
Ranar Asabar 11 ga watan Maris
- Real Madrid da Espanyol
- Elche da Real Valladolid
- Celta Vigo da Rayo Vallecano
- Valencia da Osasuna
Ranar Lahadi 12 ga watan Maris
- Real Mallorca da Real Sociedad
- Sevilla da UD Almeria
- Villarreal da Real Betis
- Athletic Bilbao da Barcelona









