Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gidan da ya fi kowanne yawan 'aljanu' a Birtaniya
Ku latsa hoton da ke sama don kallon biidyon:
Wata mata da ke zaune a wani gida da ya fi kowanne yawan ƙwanƙwamai a Birtaniya ta ba da labarin irin jiye-jiye da gane-ganen da ta dinga yi ita da iyalanta da suka sa suka bar gidan.
Da farko Liz Rich da mijinta Bill sun sa ran cewa gidan nasu da yake cikin wata gona a wajen gari a Wales zai zamo musu mai dadin zama.
Amma bayan jiye-jiye da gane-gane kamar na aljanu da suka dinga yi ciki har da ji musu rauni da ake a zahiri, sai suka kira wani fasto don yi musu addu'ar korar aljanu,
Amma duk da haka babu abin da ya sauya.
Don haka a ƙarshe sai tashi suka yi suka bar gidan.