Yadda Kiristoci suka gudanar da bikin Kirsimeti a Tudun Biri

Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama don kallon bidiyon
Yadda Kiristoci suka gudanar da bikin Kirsimeti a Tudun Biri
An wallafa

Al'ummar Kirista a garin Tudun Biri sun bi sahun Kiristoci a faɗin duniya wajen gudanar da shagulgulan bikin Kirsimeti na bana.

Albarkacin ranar ne ma, gwamnatin jihar Kaduna ta aika ayarin jami’anta zuwa garin don taya su murna, da kai musu kayan tallafi.

Hakan na zuwa ne mako uku bayan mummunar harin jirgin sojoji da ya halaka fararen hula.