Sarauniyar Netherlands da masu goyon bayan Falasɗinawa cikin hotunan Afika

An wallafa

Kamar kowane mako, a yau ma mun tattaro muku wasu daga cikin ƙayatattun hotunan Afirka da na 'yan nahiyar a wasu sassan duniya

,

Asalin hoton, Feisal Omar/Reuters

Bayanan hoto, Wata mata 'yar ƙasar Somaliya ta halarci zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawan Gaza, yayin da rikici tsakanin Isra'ila da Hamas ke ci gaba da zafafa
.

Asalin hoton, Amr Abdallah Dalsh/Reuters

Bayanan hoto, Daruruwan magoya bayan ƙungiyoyin Al Ahly ta Masar da Simba SC ta Tanzaniya ne suka kalli wasan da ƙungiyoyin suka buga cikin makon nan a gasar zakarun Afirka
.

Asalin hoton, Patrick van Katwijk/Getty Images

Bayanan hoto, Sarauniya Maxima ta Netherlands ke gaisawa da wata ƙaramar yarinya a lokacin wata ziyara da sarauniyar ta kai birnin Nairobi na ƙasar Kenya.
,

Asalin hoton, Monicah Mwangi/Reuters

Bayanan hoto, Wani mai rawar kan layi, Drady Amani ke rawa a wata unguwa a birnin Nairobi na ƙasar Kenya.
.

Asalin hoton, Monicah Mwangi/Reuters

Bayanan hoto, ...yayin da waɗannan yaran ke kallonsa
.

Asalin hoton, Emanuel Osodi/Getty Images

Bayanan hoto, Wani mutum a kan babur na kan hanyar, yayin da ambaliyar ruwa ta mamaye jihohin Ogun da Legas da ke kudu maso yamacin ƙasar.