Abin da ke haifar da ruwan ƙwallon ƙanƙara da yadda yake ƙaruwa a duniya

An wallafa

Wata mummunar dusar ƙanƙara da ta dinga faɗowa a yankin Catalonia da ke arewacin Sifaniya ranar Talata ta kashe wani jariri ɗan wata 20 da haihuwa sakamakon raunin da ya ji a kansa.

Wasu daga cikin dunƙulen ƙanƙarar da suka faɗo sun kai tsawon 10cm, inda ta dinga fasa tagogi da rufin gidaje tare da lalata layukan lantarki.

Ruwan ƙanƙarar ya kai minti 10 ana yi a lardin Girona kuma ya jikkata mutane da dama.

Maƙalar da wakilin BBC David Hambling ya rubuta a watan Maris na wannan shekara, ta duba dalilin da ya sa ake yawan samun ruwan ƙanƙarar.

____________________________________________________________

Da yammacin ranar 21 ga watan Yulin 2021, ƙwallayen ƙanƙara suka fara sauka daga sama a kan Leicestershire da ke tsakiyar birnin Landan, inda suka dinga fasa tagogi da ragargaza motoci.

Mutanen da suka fita zuwa wuraren shaƙatawa a wannan yammaci sun ƙare da yin takansu sakamakon ruwan da ya tarwatsa su.

Yayin da ruwan ƙanƙarar - da ake samu sakamakon taruwar tarin hadari a sama - ba a saba ganin irinsa ba, ba ta kai wadda aka taɓa gani ba a Calgary na ƙasar Kanada a watan Yunin 2020.

Ƙwallayen ƙanƙara masu girman ƙwallon wasan tennis sun lalata aƙalla gidaje da motoci 70,000, suka lalata amfanin gona kuma suka bar yankin cikin asarar kadara ta kusan dala miliyan 940. Ƙanƙarar da ta ɗauki minti 20 tana zuba, na cikin mafiya munin yanayi da aka taba gani a ƙasar.

Kazalika, sauyin yanayi na sauya yadda zubar ƙanƙarar yake. A Texas da Colorado da Alabama na Amurka, an samu mafi yawan ruwan ƙanƙarar da aka taba yi a tarihi, inda mai girman 16cm ta dinga zuba. A 2020, ƙanƙarar mai griman kusan 18cm ta zuba a birnin Tripoli na Libya.

Amma me ya sa ɗumamar yanayi ke haddasa ƙaruwa a yawan ƙanƙarar da ke zubowa daga sama? Kuma ko akwai iyakar girman ƙanƙarar da ya kamata ta zubo ɗin?

Nauyi, girma da kuma sauri

Ɓurɓushin ƙanƙarar da take zubowa a matsayin yayyafi, su ne suke komawa sama kuma su zama tsawa.

Iskar da take komawa sama ce ke kwashe su zuwa can inda ake da iska mai sanyin da za ta iya ƙanƙarar da su.

Sai danshin da iska ke ɗauke da shi ya taru yayin da take tafiya a cikin iskar, abin da ke sa ƙanƙarar da girma kamar na albasa.

Yawan danshin da ake da shi a cikin iska ne yake fayyace irin girman da ƙanƙarar da ke faɗowa. Za ta ci gaba da girma har sai iskar da ke kai su sama ta rage ƙarfin da za ta iya riƙe su a saman.

Iskar da ke zuwa sama mai gudun kilomita 103 cikin awa ɗaya (103km/h), ita ce ke sa ƙanƙara ta kai girman ƙwallon wasan golf, yayin da wadda ta fi haka da kashi 27 cikin 100 kan sa ƙanƙarar ta kai girman ta wasan baseball, a cewar cibiyar US National Oceanic and Atmospheric Administration (duk da cewa girman ƙanƙarar da muke gani a yanzu ba koyaushe ne take dacewa da nauyinta ba).

Yawan raɓar da iska ke ɗauke da ita da kuma yawan iskar da ke komawa sama ne ke nuna irin girman da ƙanƙarar da za ta faɗo. Mafi yawan lokaci manyan ƙanƙara kan faɗo a kusa da iskar sama yayin da ƙananan kan faɗo a can gefe.

Abin da ke haifarwa

Ƙwallon ƙanƙarar da ke faɗowa masu girman da ya wuce 25mm a girma na buƙatar wani yanayi na musamman, a cewar Julia Brimelow, wani ƙwararre kan kimiyyar fili a sashen Environment and Climate Change Canada na gwamnatin Kanada, wanda ya yi nazari kan yadda sauyin yanayi ke shafar ruwan ƙanƙara.

Suna buƙatar isasshen danshi, da iskar sama mai ƙarfi, da kuma "abin da zai jefo su", kamar dai wani yanayi na musamman.

Wannan dalili ne ya sa ake yin ruwan ƙanƙarar a wasu keɓantattun yankuna kamar Great Plains na Amurka da Gold Coast na Australia.

Waɗannan yankuna na da sanyi, da busasshiyar iska da ke sararin samaniya kuma me ɗan ɗuni, da kuma yanayin raɓa. Wannan yanayi maras kan gado na jawo iskar da ke komawa sama ta zama mai ƙarfi kuma ta haifar da tsawa.

Irin waɗannan yankuna na cikin haɗarin wani nau'in tsawa da ake kira supercells a turance, wadda ka iya haddasa babbar ƙnƙara saboda yawan jujjuyawar iskar da ke komawa sama.

Yayin da sauyin yanayi ke shafar ɗumin duniyar Earth, haka ma danshin da ke cikin iskar sama. Iskar mai ɗumi kan riƙe ruwa mafi yawa yayin da yanayi mai zafi ma ke nufin ana ƙona ruwa mafi yawa daga ƙasa.

Hakan na jawo ruwan sama kamar da bakin ƙarya da kuma yanayi masu tsanani a wasu yankuna na duniya.

Yayin da duniya ke ci gaba da ɗumama, wuraren da ake sa ran za a yi ruwan ƙanƙara ka iya sauyawa," a cewar Brimelow. "Wurin da a yanzu ake ganin ƙarancin danshi ne ke hana ƙanƙara ta faɗo zai iya zama mai danshi da yawa kuma daga baya a fara ruwan ƙanƙarar."

Mafi tsanani

Wata hanya da masana ke bi wajen lura da sauyin yanayi ta sa ƙwararru sun fahimci cewa yawan ruwan ƙanƙara zai fi yawa a yankin Australia da Turai, amma za a samu raguwa a nahiyoyin Kudancin Asiya da Arewacin Amurka.

Amma kuma sun fahimci cewa ruwan ƙanƙarar zai tsananta a wurare.

Girma

Cunkushewar ƙwallon ƙanƙara na shafar yadda girmanta zai kasance.

Yanayin nauyinta ne ke nuna yiwuwar faɗowarta daga cikin iska.

Kuma za ta iya faɗowa cikin sauri, saboda yanayin girman ƙwallon shi ne yanayin rashin saurin da za ta yi kafin ta faɗo.

Ƙanƙara mafi nauyi da ta taba faɗowa an same ta ne a Gopalganj na ƙasar Bangladesh a 1986, wadda ta kai nauyin 1.02kg.

Ruwan ya kashe mutum 40 tare da raunata wasu 400, a cewar rahotanni na lokacin, amma daga baya an ce kusan 92 ne suka mutu.

Amma wane irin girma ƙanƙarar ke da ita?

Irin girman da za su kai

Masanin yanayi Matthew Kumjian daga Jami'ar Jihar Pennsylvania ya yi ƙiyasin mafi tsawon ƙanƙarar ita ce 27cm - wadda ta fi ƙwallon ƙafa girma - bisa tsarin neman bayanai.

Sai dai kuma, har yanzu ba a sake ganin irin wannan ƙanƙarar ba amma ya ce yana aiki da abokan aikinsa don sake ƙiyasin.

Duk da cewa 27cm ne mafi girman, irin wannan ƙanƙarar ka iya zama marasa takamaiman zubi.