Mata ne za su yi rafli a wasan Costa Rica da Jamus a Qatar 2022

An wallafa

Za a kafa tarihi a wasan Costa Rica da Jamus a Gasar Kofin Duniya, inda Stephanie Frappart za ta zama ta farko da za ta yi rafli a karawar maza.

Costa Rica da Jamus za su fafata ranar Alhamis 1 ga watan Disamba a wasa na uku-uku a rukuni na biyar da za su kara a filin wasa na Al Bayt.

Mata uku ne za su ja ragamar wasan a ranar a kuma karon farko da mata za su hura wasan Gasar Cin Kofin Duniya a tarihin wasannin da aka fara 1930.

Wadanda za su taimaka mata aiki sun hada da Neuza Back da kuma Karen Diaz.

Wannan ba shi ne karon farko da Frappart, mai shekara 38 za ta hura babban wasan tamaula ta maza ba, bayan da ta yi rafli a Ligue 1 da kuma Champions League.

''Wasan maza a Gasar Kofin Duniya yana da mahimmaci - ni ce ta farko daga Faransa da kuma Turai da zan yi alkalanci, saboda hada na san yadda zan hura karawar,'' in ji Frappart.

Kafin fara Gasar Cin Kofin Duniya a Qatar, shugaban kwamitin alkalan Fifa, Pierluigi Collina ya ce ''Alkalan uku da aka zaba, ba an gayyace su bane don suna mata, sai don raflin Fifa ne. Za su hura kowanne iri wasa a Qatar.''

A rukuni na biyar Sifaniya ce ta daya da maki hudu, sai Japan da Costa Rica masu maki uku-uku kowacce da kuma Jamus mai maki daya kwal.