'Ɗan uwana ya ceci rayuwata, amma ya rasa ransa'

    • Marubuci, Jonathan Beale
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Tomakivka
  • An wallafa

Maksym ya shafe sa'a 200 ana gwabza fada da shi ba tare da hutu ba kafin aka kashe shi a birnin Bakhmut.

"Tsawon kwana takwas bai ci abinci ba," kamar yadda mahaifiyarsa Lila ta bayyana. Ya ma kasa rufe idonsa tsawon minti biyar saboda harbin.

Akwai dalilin da ya sa yanzu take kiran Bakhmut "jahannama". Birni ne da ya yi sanadin ɗaukar rayuwar ɗanta ɗaya kuma ɗayan ya ji rauni sosai.

Halin da ta shiga shi ne - ɗanta ɗaya ya rasu yayin da take ƙoƙarin ceto ran ɗayan.

Maksym da Ivan sun amince su shiga yaƙi lokacin da Rasha ta afka wa Ukraine a bara.

A lokacin Maksym yana da shekara 22 yayin da Ivan ke shekara 18.

Ivan, wanda shi ne ƙarami ya ce sun shaƙu sosai. "kullum muna tare. Ina ɗaukarsa mai matuƙar muhimmanci."

Faɗan da aka gwabza gida-gida a Bakhmur ne lokaci na ƙarshe da suka kasance a tare. "Abu ne mai wahala yin bacci a can. Ana kai mana hari dare da rana," in ji Ivan.

Ƴan uwan sun maƙale ne cikin wani ɗaƙi da ba shi da taga. Dole sai da suka fasa bango domin samun damar harbi. A lokacin ne suka samu umarnin su janye.

Ivan ya bayar da labarin halin da ya shiga lokacin da ya ji rauni. "Na tuna ina ƙoƙarin loda bindiga, na fito gefen bango kuma akwai haske, Na fita hayyacina kuma na faɗi"

Ya ce daga nan ya ji ɗumin jini da ke kwarara daga raunin da ya samu a fuskarsa. Bai yi tunanin zai rayu ba. "Na yi tunanin na tafi ke nan, sai jini ke zuba"

Amma Maksym ya fito a guje domin cetonsa ya ja shi cikin ginin domin samun mafaka.

"Ya farfaɗo da shi, ya cire min hakorin da ya ɓalle ya fara ba ni kulawar gaggawa," in ji Ivan.

Ivan ya nuna wani bidiyon ɗan uwansa da ke share jini bayan harin.

Wani bidiyon ya nuna Ivan yana koƙarin tafiya cikin rauni, kuma riƙe da tutarsa ta Ukraine: alama ta jarumta da turjiya a fagen daga a Bakhmut.

Ivan bai taɓa tunanain zai rayu ba idan ba don ƙoƙarin Maksym ba. "Ɗan uwana ya yi ƙoƙarin ganin ban mutu ba. Ya ceci ni."

Nan take Maksym ya yi kiran neman taimako. Amma jami'an lafiya da suka yi ƙoƙarin samunsa duk an kashe su a motarsu da harin rasha ya rutsa da su. An ɗauki awa tara kafin a ceto Ivan.

Daga nan Maksym ya nuna jarumta. Maimakon tafiya tare da ɗan uwansa don tsira, ya gwammace ya tsaya a Bakhmut, domin jagorantar tawagarsu.

Ya ci gaba da fada bayan sati ɗaya aka kashe Maksym.

A Ukraine jana'izar sojoji ta zama kusan kullum. Amma dukkaninsu ba za a kwatanta su da Maksym ba. Tare da iyalinsa, dukkanin al'ummar Tomakivka sun fito domin girmama shi.

Sun durƙusa a lokacin da ake wucewa da gawarsa zuwa maƙabarta - wasu suna ajiye furanni ko kuma tutar Ukraine. Daga baya aka yi addu'o'i da kiɗa sai kuma kuka da jimami suka biyo baya.

Tsawon shekaru, iyayen Maksym da Ivan na cike da damuwa kan yaƙin da suka shiga. Lilia da Serhii ba su iya bacci - suna jiran ji daga ƴan uwansu. Sukan tura masu da saƙo, in ji Lilia - "Muna nan ƙalau, mama."

Amma daga baya sai labari ya same su.

Lilia ta yi kuka sosai a jikin akwatin gawar Maksym kafin a binne shi - wadda aka yi wa harbi bindiga na karramawa. "Mun kasa yarda har yanzu. Rayuwata ta kaɗu," kamar yadda Lilia ta shaida min bayan jana'izar. Ta ce dalilinta kawai na rayuwarta shi ne don rayuwar sauran ƴaƴanta.

Ta faɗa min cewa Maksym yana da damar rayuwa da Ivan, amma ba zai manta da ƙannensa ba.

"Jarumi ne, tauraro ne. Ba zai taɓa barin ɗan uwansa ba duk da ya san cewa shi ma zai mutu."

Ukraine ta kasa faɗin adadin yawan mutanen da aka rasa a wannan yaƙin. Amma idan ka duba maƙabarta za ka fahimci cewa ɗaukacin ƙasar na cikin tashin hankali.

A wannan ƙaramin kaɓarin, a wannan ƙaramin garin, akwai jerin ƙaburbura da aka kewaye da faranni. Maksym na ɗaya daga cikin sojoji uku da wani limamin soji ya yi wa jana'iza a makon.

A wajen jana'izar, Ivan yana riƙe da tutar Ukraine wadda yake riƙe da ita lokacin da ya ji rauni - Jinin raunin da ya ji ya ɓata kore da ɗoruwa na tutar.

Na tambaye shi ko ya yi nadamar shiga soja. Ya amsa da cewa: Mun fahimci cewa ba za mu dawo ba, amma babbar karramawa ce yi wa Ukraine yaƙi. Shi ya sa ba zan taɓa yin nadama ba.

Ɗan uwana ya sadaukar da rayuwarsa don ƙwato ƴancinmu. Amma ƴanci ba ya samuwa sai da zubar da jini.