An raba maki tsakanin Barca da Man United a Nou Camp

An wallafa

Barcelona da Manchester United sun tashi 2-2 a wasan farko a neman matakin shiga Europa League gurbin 'yan 16.

Minti biyar da komawa zagaye na biyu Barca ta zura kwallo ta hannun Marcos Alonso, sai dai minti uku tsakanin Marcus Rashford ya farke.

Daga baya Barca ta ci gida ta hannun Jules Kounde, kafin Raphinha ya farke.

Wasa na 24 da suka fuskanci juna, inda Barce ta ci shida da canjaras biyar, United ta yi nasara a uku.

Sun kara a bana ne, bayan da Barcelona ta kasa kwazo a Champions League a cikin rukuni, karo na biyu kenan a jere.

Ita kuwa United ta yi wasan, bayan da ta yi ta biyu a cikin rukuni a Europa League, dalilin da ta fuskanci Barca kenan, don samun gurbin buga zagayen 'yan 16.

United za ta fafata da Leicester City ranar Lahadi, sannan ta karbi bakuncin Barcelona ranar Alhamis.

Daga nan kungiyar da Ten Hag ke jan ragama za ta buga wasan karshe a Carabao Cup da Newcastle a Wembley.

Rabon da kungiyar Old Trafford ta lashe kofin tun na Europa League da ta dauka a 2017 karkashin Jose Mourinho.

Ita kuwa Barcelona wadda ta bai wa Real Madrid tazarar maki takwas a La Liga za ta karbi bakuncin Cadiz, sannan ta ziyarci Ingila.