Roger Federer zai yi ritaya a karshen watan Satumba

Federer ya gaza buga gasa ko daya cikin shekarar nan, sakamakon ciwon gwiwa da yake fama da shi

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Fitaccen dan wasan Tennis dinan dan kasar Switzereland Roger Federer, ya sanar da shirinsa na yin ritaya daga wasan, a karshen wannan watan.

 Dan wasan da ya lashe gasar Grand Slam sau 20 a tarihi, bai buga wasa ba tun gasar Wimbledon da aka yi a 2021, bayan aikin da aka yi masa a gwiwarsa karo na uku a tarihi.

 Ya ce "ya buga wasanni sama da 1,500 a cikin tsawon shekara 24. don haka jiki ya nuna gazawa dole na hakura da buga gasa. "

 Ya kara da cewa: " Ga was an Tennis, Ina son wannan was an kuma ba zan taba barinsa ba. "

 Sama da shekara uku Federer na fama da ciwon gwiwa, wanda hakan ya sa ya buga gasar Grand Slam uku kacal cikin 11 tun farkon 2020.

Bai buga wani wasan azo a gani ba tun wasan da ya yi rashin nasara a hannun Hubert Hurkacz a wasan kusa da na karshe a gasar Wimbledon a bara.

Sannan ya sanar da cewa yana bukatar a yi masa tiyata a gwiwarsa, bayan biyu da aka yi masa a 2020.