Ƙa’idoji da muhimmancin azumin Sitta Shawwal a Musulunci

Bayanan bidiyo, Taɓa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Ƙa’idoji da muhimmancin azumin Sitta Shawwal a Musulunci
An wallafa

Bayan wucewar azumin watan Ramadan, Musulmai kan yi wani azumin na kwana shida a cikin watan Shawwal. Shi ne azumin da ake kira Sitta Shawwal, domin dacewa da tarin ladan da ke tattare da su.

Malaman addinin Musulunci sukan ambato wani Hadisi daga Manzon Allah (S.A.W) da ke cewa duk wanda ya azumci watan Ramadan sannan ya ƙara da azumin kwana shida cikin watan Shawwal, to za a rubuta masa ladan wanda ya shekara yana azumi.

Malam Tukur Adam wani malamin addini a Najeriya ya ce ana so mutum ya fara biyan bashin azumin da ake bin sa, kafin yin Sitta Shawwal, matuƙar zai iya yin su kafin ya yi Sitta Shawwal.

Amma ya ce matuƙar azumin da ake bin mutum yana da yawa, ta yadda ba lallai ne ya iya biya gaba ɗaya a watan Shawwal ba, to ya fara yin na Sitta Shawwal ɗin, kasancewar na Sitta Shawwal ɗin suna da ƙayyadajjen lokaci.