Muna jiran gwamnati kan alawus ɗin masu yi wa ƙasa hidima - Shugaban NYSC

Muna jiran gwamnati kan alawus ɗin masu yi wa ƙasa hidima - Shugaban NYSC
An wallafa

Shugaban hukumar yi wa ƙasa hidima ta Najeriya, NYSC Birgediya Janar Yusha'u Dogara Ahmed ya shaida wa sashen Hausa na BBC cewa har yanzu ba su ji komai daga gwamnati ba.

"To ai ko ama'aikatan gwamnati da aka bai wa albashi mafi ƙaranci ya ɗauki lokaci kafin a fara biyan su. Mu ma muna jira. Yaya za su tsara? Muna nan muna jiran su. A duk lokacin da gwamnati ta kammala komai za ku ji sannan su ma masu yi wa ƙasa hidimar za su ji labari." In ji Birigediya Janar Yusha'u Dogara Ahmed.

Masu yi wa ƙasa hidima a Najeriya na ci gaba da darawa har kunne, tun bayan da gwamnatin ƙasar ta sanar da yi musu ƙari a kudin alawus ɗinsu.

A ranar Laraba ta 25 ga watan Satumba ne dai gwamnatin ƙasar ta sanar da yi wa masu yi wa ƙasa hidimar ƙari a alawus ɗinsu zuwa naira 77,000.

Wata sanarwa da kakakin hukumar NYSC, Caroline Embu ta fitar, ta ce ƙarin zai soma aiki daga watan Yulin da ya gabata.

Sanawar ta ƙara da cewa an yi ƙarin alawus ɗin ne saboda ƙarin mafi ƙanƙantar albashi da gwamnatin Najeriya ta yi.